Babban adalcin da za a yi wa sojojin Najeriya da tsagerun Delta suka kashe, shi ne ko ta halin ƙaƙa a tabbatar da kamo makasan, kuma a hukunta su. Ta haka ne za a iya kawo ƙarshen irin wannan mummunan kisan dabbancin da aka yi wa jami’an tsaron da ke sadaukar da rayuwar su wajen kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya.
Ɓoyayyun hujjoji sai ƙara bayyana suke yi, dangane da mummunar ranar da matsalar tsaro ta ƙazamce ƙasar nan, yayin da aka yi wa sojojin Najeriya su 17 mummunan kisan gilla, a hannun tsagerun ƙauyen Okuama cikin Jihar Delta, a ranar 14 Ga Maris.
Ba mummunan kisa kaɗai aka yi wa sojojin ba, bayan an kashe su, an guntule kawunan 14 daga cikin su. Kuma aka farka cikin su, aka fizgo zuciyar kowanen su. Ba a nan wannan dabbanci ya tsaya ba. Sun kuma bi gawarwakin sojojin ɗaya bayan ɗaya sun guntule al’aurar su. Ƙololuwar kisan dabbanci kenan.
Yayin da wannan bala’i ya zo daidai lokacin da masu garkuwa da kuma Boko Haram ke ƙara maƙasura, inda aka sace sama da mutum 500 na ɗalibai da masu gudun hijira a Kaduna da Barno, hakan na nuni da irin jan aikin da ke gaban manyan jami’an tsaron ƙasar nan.
Amma kuma babban darasin da kowa zai ɗauka a wannan mummunan yanayi, shi ne, ba wanda zai iya bugun ƙirji ya ce shi dai wannan abu ba zai iya ritawa da shi ba.
Tun daga Shugaban Ƙasa har Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa da ɗaukacin ‘yan Najeriya sun kaɗu sosai da wannan dabbanci da aka yi wa sojojin Najeriya. Kuma kiran da kowa ke yi shi ne, tilas a kamo waɗanda suka yi wannan mummunan aiki, kuma tilas a hukunta su.
Saboda hukunta su shi ne babban bashin da Najeriya za ta iya biya ga iyalan sojojin 17 da aka yi wa mummunan kisa.
Daga cikin waɗanda aka kashe ɗin har da Laftanar Kanar A.H Ali, Kwamandan Bataliyar A-yi-ta-ta-ƙare ta 181, Manjo-manjo biyu da Kaftin ɗaya.
Ba kamar irin kisan da aka taɓa yi wa sojoji a yankin Shiroro a Jihar Neja ba, cikin Agusta, 2023, inda aka kashe soja 22, suka aka yanka su kamar kaji yayin da suka kai wani farmaki, to su sojojin da aka kashe a Delta sun je ne domin wanzar da zaman lafiya a yankin ƙauyen Okuama, bayan faɗa ya ɓarke kan rikice-rikicin gona tsakanin ƙabilun Okuama da Okolaba.
Abin takaici waɗanda suka kashe sojojin sun hana zaman lafiya samuwa a ƙauyen. Saboda kowa ya gudu, wasu sun koma maƙwautan ƙauyuka, wasu na ta watangaririya a cikin daji. Ba su san abin da zai je ya dawo ba. Ba su san ranar da ƙurar za ta lafa ba. Amma dai ko za ta lafa, to ba yanzu ba.
Sai dai abubuwan da suka biyo baya na banka wa garin wuta ya ƙone ƙurmus, nesanta kan su da sojoji suka yi kan zargin kai ƙone garin da kuma iƙirarin da Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi cewa kisan da aka yi wa sojojin mutanen garin ne suka tsara komai, hakan na nufin a maganar ramuwar-gayya, abin zai iya shafar waɗanda ba su da hannu kwata-kwata a kisan.
Amma dai mu a na mu ra’ayin, irin wannan ta’addanci wasu tsirarun kangararru ne ke shirya shi.
Ko ma dai me kenan, ya kamata sojoji su yi taka-tsantsan wajen tabbatar da sun kamo waɗanda suka yi wannan aika-aika.
Dangane da wannan kisan gillar da tsagerun Delta suka yi wa sojojin Najeriya, PREMIUM TIMES na mai ra’ayin cewa babban adalcin da za a yi wa sojojin Najeriya da tsagerun Delta suka kashe, shi ne ko ta halin ƙaƙa a tabbatar da kamo makasan, kuma a hukunta su. Ta haka ne za a iya kawo ƙarshen irin wannan mummunan kisan dabbancin da aka yi wa jami’an tsaron da ke sadaukar da rayuwar su wajen kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya.
Discussion about this post