Gwamnonin PDP da kuma ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Legas sun bada shawarar a kafa ‘yan sandan jihohi, domin magance gagarimar matsalar tsaron da ta dabaibaye faɗin Najeriya.
Gwamnonin sun fito da wannan matsaya ta su bayan kammala wani taro da suka yi a Abuja, a ranar Litinin.
Su ma ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Legas, sun amince da shawarar da aka bayar bayan zaman su na ranar Litinin cewa ya zama wajibi kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta, domin a haɗa ƙarfin daƙile matsalar tsaro, wadda a kullum ta ke ƙara taɓarɓarewa.
Bayan sun tashi daga taron, Gwamnonin PDP sun fitar da matsayar su da ke ƙunshe a cikin takardar bayan taro cewa za su ci gaba da bayar da gudummawa da goyon bayan ganin an magance matsalolin tsaro da kuma kawo sauƙi ga rayuwar ‘yan Najeriya.
Sannan kuma sun sun sake jaddada kiraye-kirayen buƙatar kafa ‘yan sandan jihohi.
Sai dai kuma sun kawo tsokaci dangane da yadda za a kafa su domin a guji yin amfani da su ba ta hanyar da ta dace ba.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da na Bauchi, Bala Mohammed, Siminalayi Fubara na Ribas, Seyi Makinde na Oyo, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Dauda Lawal na Zamfara, sai kuma Kefas Agbu na Taraba.
Sauran sun haɗa da Godwin Obaseki na Edo, Mataimakin Gwamnan Enugu, Ifeanyi Ossai, sai Mataimakin Gwamnan Delta, Monday Onyeme.
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP.
Bala ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tsayar da taɓarɓarewar darajar naira.
Sannan kuma ya kira ga gwamnatin tarayya ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin a bijiro da hanyoyin sauƙaƙa wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.
Discussion about this post