Yanzu hankali ya kwanta a Jihar Kano, bayan da Gwamna Abba Yusuf ya samu nasarar tabbatar masa da lashe zaɓen 2023 da ya yi.
Akwai batutuwa 30 dangane da wannan shari’a, waɗanda yawanci aka bijiro da su, kafin a soke nasarar da kotunan baya suka ɗirka wa Nasiru Gawuna na APC.
1. Nasiru Gawuna ba ya cikin masu shigar da ƙara. APC ce ta shigar da ƙara, bayan Gawuna ya karɓi ƙaddara da farko, har ya taya Abba Gida-gida murnar lashe zaɓe.
2. Ƙuri’un da Abba ya samu sun kafa tarihi, domin a tarihin zaɓen Najeriya, ba a taɓa samun ɗan takarar gwamna da ya samu ƙuri’u miliyan ɗaya ko miliyan 1 da ɗoriya ba, sai Abba.
Kotun Ƙoli:
3. Alƙalai 5 na Kotun Ƙoli duk sun yarda cewa shari’u biyu na baya da aka soke nasarar Abba, ba daidai ba ne, duk sun yi fatali da shari’un.
4. Jagoran Alƙalan, Babban Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tafka babban kuskure da har ta jaddada hukuncin soke zaɓen Abba da Kotun Zaɓen Kano ta yi.
5. Shari’ar zaɓen gwamnan Kano ce kaɗai shari’ar da Kotun Ƙoli ta soke hukuncin kotunan baya a zaɓen 2023.
6. Okoro ya yi kakkausar suka sosai kan soke zaɓen Abba da Kotun Zaɓen Kano ta yi.
7. Kotun Ƙoli ta ragargaji yadda Kotun Zaɓen Kano ta zabtare wa Abba ƙuri’u 165,616.
8. Ta ce Abba cikakken ɗan jam’iyyar NNPP ne kafin a yi zaɓen gwamna.
9. Kotun Ƙoli ta ce ayyana cewa Abba ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da aka gudanar da zaɓen gwamna, babban kuskure ne dabai kamata a yi Kotun Zaɓen Kano ta tafka ba. Kuma bai dace a ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada ɗanyen hukuncin ba.
10. Kotun Ƙoli ta ce batun fitar da ɗan takara matsalar jam’iyya ce a cikin gida.
11. Kotun Ƙoli ta ce duk mai jayayya da takarar wanda ya yi nasara, to kafin zaɓe ake yi, ba bayan zaɓe ba.
12. Mai Shari’a Okoro ya koro bayanin cewa Sashe na 177(c) na Dokar Zaɓe, ya yi hani ne kawai ga ɗan takara ya tsaya takara indifenda, ba tare da shiga wata jam’iyya ba.
13. Kotun Ƙoli ta ce laifi ne babba ga wata kotu ta binciki batun takarar wani bayan an kammala zaɓe. Don haka Kotun Zaɓen Kano ta yi babban laifi, haka ita ma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi kuskure da ta jaddada amincewar ta kan binciken mamba ko rashin mamba ɗin Abba a NNPP.
14. Batun ƙuri’u 165,616 da Kotun Zaɓen Kano ta zaftare wa Abba, Kotun Ƙoli ta ce ai ko na sitamfi ƙuri’un sun zama sahihai, tunda INEC ta ce nata ne. Kuma APC ba ta kawo hujjar cewa ba na INEC ɗin ba ne.
15. Kotun Ƙoli ta gargaɗi kotuna su riƙa bibiyar ƙararraki a natse, su guji aiwatar da hukuncin da zai kawo ruɗu a cikin jama’a.
16. Kotun Ƙoli ta ce, “kan wane dalili jam’iyyar APC za ta ƙalubalanci ƙuri’un Abba, bayan wakili ko ejan ɗin ta ya amince har ya sa hannu a rumfar zaɓe?
17. Kan me APC za ta ƙalubalanci ƙuri’un Abba bayan ejan ɗin ta ya amince, ya sa hannu a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe? To don me za ta je kotu ta yi ƙorafi kuma?
18. Kotun Ƙoli ta ce ta yi fatali da hukuncin soke zaɓen Abba da Kotun Zaɓen Kano ta yi.
19. Kotun Ƙoli ta ce ta yi fatali da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadda ta jaddada hukuncin soke zaɓen Abba.
20. Kotun Ƙoli ta ce Abba ne ya yi nasara a zaɓe, kuma shi ya yi nasara a kotu.
Discussion about this post