Matatar Ɗangote ta fata tace dizal da man jiragen sama. Haka dai wata sanarwa ta bayyana daga masana’antar a ranar Juma’a.
Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da irin goyon bayan da ya ba shi da kuma ƙwarin-guiwa da shawarwari har wannan gagarimin aiki ya tabbata.
Dangote ya kuma gode wa NNPC Limited, NUPRC da NMDPRA.
“Wannan babbar rana ce mai ɗimbin tarihi da matuƙar muhimmanci ga Najeriya. Hakan na nuni da cewa za mu iya bunƙasa ƙasar mu tunda har muna iya kafa katafariyar masana’anta kamar wannan.”
Sanarwar ta ce zuwa yanzu masana’antar ta karɓi ɗanyen mai ganga miliyan 6, daga ranar 12 ga Disamba 2023 zuwa 8 ga Janairu, 2024.
Matatar Ɗangote za ta iya loda tankar mai 2,900 a kowace rana. Kuma man da ya fara tacewa ya na nagartar da dukkan ƙasashen Turai ke buƙata.
An gina matatar bisa tsari da ƙa’idojin da Bankin Duniya, US EPA da sauran ƙa’idojin da duniya ta yarda da su dangane da kauce wa fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli.
Sannan kuma an gina ta da kayan aiki na zamani.
Kamfanin Ɗangote ya gode wa bankuna, ma’aikata, gwamnatin Jihar Legas da sauran waɗanda suka sa himma domin tabbatar da ganin ma’aikatar ta fara aiki.
Discussion about this post