Fadar Shugaban Ƙasa ta fesa wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar zafafan kalamai, inda ta ce furucin sa kan Shugaba Bola Tinubu akwai kasassaɓa da gwatson-zance a ciki.
Idan ba a manta ba, Atiku ya yi kira ga Shugaba Tinubu da cewa bai yiwuwa yayin da ƙasa ke fama da matsalar tsaro, shi kuma sai bulkara da gallafirin yawon biɗar-kaɗe ya ke ta yi cikin duniya.
Atiku ya ce Tinubu ya nuna ba ya iya riƙe Najeriya. Tunda ragamar ya fi ƙarfin sa, don haka ya sauka daga mulki kawai, tunda shugabancin Najeriya ba gadon gidan su ba ne.
“Idan takalmin Najeriya sun fi ƙarfin Baba Emilokan, sai ya sauka kawai, domin da asara ai gara gidadanci. Najeriya ba ta buƙatar wani talasurun shugaban ƙasa, wanda bai san komai ba sai yawo kaɗai.
“Ƙasar nan ta na buƙatar shugaba wanda zai iya aiki 24/7, ta yadda zai tunkari matsalar tsaro gadan-gadan.”
Sai dai kuma Mashawarcin Shugaba Tinubu na Musamman kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana kalaman Atiku cewa akwai “kasassaɓa da sakin baki a ciki.”
Onanuga ya ce duk da Shugaba Tinubu ya na ƙasar Faransa, amma ya na bibiyar dukkan abin da ke faruwa a ƙasar nan.
Kalaman Atiku sun zo ne daidai lokacin da wata ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyi 48 suka yi kira ga Shugaba Tinubu ya kafa dokar-ta-ɓaci kan matsalar tsaro.
Haka kuma a ranar Talata ce Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya yi kira ga Tinubu a yi garambawul a fannin masu ruwa da tsakin matsalar tsaro, domin a cewar sa, tsarin da ake a kai a yanzu da nufin kawar da matsalar tsaro, ba shi da wani tasiri, sai a sake dabara.
Discussion about this post