Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya bayyana a ranar Talata cewa Majalisar Tarayya za ta yi Taro na Musamman dangane da gagarimar matsalar tsaron da ta addabi Najeriya baki ɗaya.
Ya bayyana haka yayin da aka koma zaman majalisa, inda ya ke cewa matsalar tsaro a ƙasar nan ta yi muni kuma ta ƙazanta matuƙar gaske.
“Ina bada shawarar gudanar da Taron Majalisar Tarayya kan Matsalar Tsaro. Taron zai kasance ya zama wurin da za a bijiro da shawarwari daga bakin masu ruwa da tsaki a ɓangarori da dama, kamar jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, malaman addini, masana daga jami’o’i da cibiyoyin ilmi, ƙungiyoyi da sauran su.”
Abbas ya ce hakan zai “shimfiɗa miƙaƙƙar hanyar da za a bi domin a kawo ƙarshen matsalar tsaro.
“Lokaci ya yi da za mu taru mu kawar da duk wata miskilar da ke kawo cikas wajen daƙile matsalar tsaro. Idan mun yi haka, za mu wanzar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a ƙasar nan,” inji shi.
Abbas ya ce maganar gaskiya da tsarin da a yanzu ake kai wanda ake bi don ganin an daƙile matsalar tsaro, ba shi da wani tasiri.
Daga nan sai ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya tashi tsaye ya sauya tsarin kwata-kwata.
Ya shawarci Tinubu ya ƙara matsa wa manyan hafsoshin tsaron ƙasa lamba, kuka idan ta kama ya ɗauki wani tsatsauran mataki a kan su, to ya gaggauta ɗauka.
“Idan ma ta kama a yi wani gagarimin garambawul a cikin manyan tsaron ƙasar nan, to a hakan, domin lamarin ya na neman gagara fa.”
A ranar Litinin ce dai wannan jarida ta buga labarin cewa wasu ƙungiyoyi 48 sun ce lokacin kafa dokar-ta-ɓaci kan matsalar tsaro ya yi, bayan kashe mutum aƙalla 2,343 a watannin mulkin Tinubu.
Wasu ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin ɗan Adam da kare dimokraɗiyya sun yi kakkausan kira ga Shugaba Bola da ya gaggauta kafa dokar-ta-ɓaci kan matsalar tsaro.
Kungiyoyin su 48 sun bayyana wannan matsaya ta su a wani taron manema labarai na duniya da suka kira a Abuja, ranar Litinin ɗin nan.
Babban Daraktan CISLAC, Auwal Rafsanjani, wanda ya yi jawabi a madadin sauran ƙungiyoyin, ya ce su na cikin nuna matuƙar damuwar su dangane da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan.
Daga nan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye haiƙan ta magance wannan matsala.
“Gangamin ƙungiyoyi a ƙarƙashin ‘Civil Society Joint Action Group, Community of Practice Against Mass Atrocities, and Nigeria Mourns, sun damu ƙwarai dangane da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan, har da Abuja, Babban Birnin Tarayya, FCT da kewaye.
“Dangane da haka ne mu ke yin kira ga Gwamnatin Najeriya ta yi gaggawar tashi tsaye ta kawo ƙarshen wannan yawan garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda, kuma a binciki yawan mutanen da suka ɓace sanadiyyar hare-haren da ake kai masu,” inji Rafssanjani.
Ya ce matsalar tsaro ta ci gaba tun daga gwamnatocin baya guda uku, ciki kuwa har da ta tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda shi tsohon Janar ɗin soja ne, wanda ‘yan Najeriya su ka damƙa masa amanar kare lafiya da rayukan su, amma hakan bai samu ba a lokacin mulkin sa.
Rafsanjani ya ce a zangon mulkin Buhari na biyu daga 2019 zuwa 2023, an kashe mutum aƙalla 24,316 a Najeriya, sannan kuma an yi garkuwa da mutum 15,597 duk a lokacin
Ya ƙara da cewa a iyakar watannin da Tinubu ya yi kan mulki daga Mayu 29, 2023 zuwa Janairu 2024 na mulkin Tinubu, an kashe mutum 2,423, sannan an yi garkuwa da mutum 1,872.
Discussion about this post