Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum,
Ƴan uwana Zamfarawa, ‘yan uwana ‘yan Najeriya, ‘yan uwana Al’ummar Musulmi baki daya. Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kare ku da mu da zuri’ar mu baki daya daga sharrin ‘yan ta’adda, da sharrin barayin daji, wadanda suka dade suna cutar da al’ummah, amin.
Kuma ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kawo muna karshen wannan mummunan ibtila’i da wannan jarabawa mai hadari ta ‘yan ta’adda da barayin daji da suka addabi garuruwanmu da al’ummominmu; kuma ina addu’a da rokon Allah ya tausaya muna, ya jikanmu, ba don halin mu ba, ya yaye muna dukkan damuwa, ya bamu lafiya da zaman lafiya, amin.
Bayin Allah masu girma, duk da cewa a gaskiya, gwamnatocin jihohin da Allah ya jaraba da wannan bala’i da ma gwamnatin tarayya suna iya kokarinsu akan wannan bala’i, kuma ana samun ci gaba sosai, to amma dai wadannan hare-hare gaskiyar magana, kullun sai kara kamari suke yi. Yadda lamarin yake shine, idan an yi kokari an toshe can, sai ka ga sun bulla wani wuri daban.
Sannan duk da cewa wadannan barayi, ‘yan ta’adda, su kan shiga cikin babban birnin jiha wasu lokuta, wato garin Gusau, su kai hare-hare, su kashe bayin Allah, su dauki na dauka, a anguwanni kamar Saminaka, Damba, Mareri, Bayan NTA, Bulunku da sauransu. To yanzu ‘yan uwa lamarin sai dada matso wa yake yi, sai kusantowa yake yi cikin babban birnin jiha, wato Gusau.
Abin da ya faru shine, shekaran jiya Juma’ah da dare, misalin karfe goma sha daya na dare, sun shiga cikin garin Gusau, a nan anguwar Danbaba, wadda aka fi sani da suna Tsunami, suka shiga gidajen bayin Allah, suka dauki wani mutum da iyalansa su shida duk mata; suka kara gaba kadan, suka shiga gidan wata baiwar Allah, ‘yar kasuwa, mai suna Uwani, suka sassari maigidanta mugun sara da adduna, don sun ma dauka cewa ya mutu, suka tafi suka bar shi jina-jina cikin jini, wanda yanzu haka yana asibiti yana karbar magani, daga asibiti kuma yau da safe an kai shi family house din su a anan Zawuya, domin samun cikakkiyar kulawa. Bayan sun sare shi, sun dauki uwargidansa, ita Uwani din, tare da mutum hudu, da ‘ya ‘yanta, duk mata, suka tafi da su.
Ya ku jama’ah, muna rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kubutar da wadannan bayin Allah, ya dawo da su cikin iyalansu, tare da dukkanin daruruwan bayin Allah da suke hannun wadannan barayi, ‘yan ta’adda, amin.
Tabbas, ko shakka babu, jami’an tsaro da Gwamnatocin jihohin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jaraba da wannan fitina, kai da ma gwamnatin tarayya, da dukkanin jami’an tsaronmu, Allah ya sani, suna iya kokarinsu a kan wannan fitintinu, amma dai duk da haka, akwai bukatar kara kaimi wurin kokarin kawo karshen wannan rikici, domin al’ummomin da suka zabe su su zauna lafiya cikin amincin Allah, kamar yadda suka dauki alkawari tsakaninsu da Allah, Mahaliccinsu.
Ya ku gwamnatoci, ina mai kara tunatar da ku abun da dama can kun san shi. Kuma Allah Subhanahu wa Ta’ala shine yayi umurni da a tunatar din, domin ita tunatarwa tana amfanar dukkan mumini, bawan Allah, mai kyakkyawar manufa zuwa ga al’ummarsa.
Ina wannan tunatarwa ce, ba domin kun kasa ba, ko kuma baku kokari ba, ko kuma baku dauki mataki ba. Allah ya sani ba haka bane. Amma dai ina tunatar da ku ne game da alkawurran da kuka dauka, tsakaninku da ubangijinku, na kare rayukan talakawan ku da dukiyoyinsu.
Ku sani, dukkanin mu zamu mutu, zamu koma ga Allah, zamu tashi gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala domin yayi muna hisabi a kan yadda muka gudanar da rayuwar mu a wannan duniya. Kuma kowannen mu, Allah Subhanahu wa Ta’ala zai yi masa hisabi, a kan dukkanin alkawurran da ya dauka; za’a tambaye shi, shin ya cika wadannan alkawurra kuwa?
Kauyukka da garuruwan jihar Zamfara suna cikin damuwa da tashin hankali. To kuma yanzu ga shi abun har ya wuce kauyuka, ya shigo cikin garin Gusau, babban birnin jiha tsundum.
Ya ku shugabannin mu, muna kira a gare ku, da ku kara kaimi wurin yakar wadannan azzalumai!
Sannan ina kira na musamman, zuwa ga mai girma Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal, gwamnan da duniya ta shaida cewa, talakawa ne suka zabe shi, kuma duniya ta shaida cewa, Zamfarawa suna kaunarsa, suna tare da shi da addu’oinsu da goyon bayansu dari-bisa-dari, da ya gaggauta, ya kaddamar da rundunar nan ta musamman, ta ‘yan sa kai, wadanda gwamnatinsa ta dauka, domin su fara aiki gadan-gadan. Domin ga shi dai, wadannan barayi ‘yan ta’adda, har zasu iya shiga cikin garin Gusau, su dauki mutane, su tafi da su daji.
Don Allah mai girma Gwamna, tabbas kuna kokari, to amma ku kara kokari, tare da fatan Allah ya taimakeku, ya sa maku hannu, ya dafa maku, amin.
Sannan na biyu, ina kira na musamman, tare da tunatarwa, ga mai girma ministan tsaro, Alhaji Bello Muhammad Matawallen Maradun, da cewa shi ma yaji tsoron Allah, kuma ya sani, wallahi kamar yadda Allah zai tambayi Gwamna Dauda Lawal, a kan lamarin tsaron jihar Zamfara, to shi ma Allah zai tambaye shi, kasancewar shi ministan tsaro a Najeriya. Domin shi ma yayi alkawari, tsakaninsa da mahallicinsa, kuma yayi rantsuwa a lokacin da Shugaba Tinubu ya bashi wannan aiki na Ministan tsaro, cewa zai kare rayuka da mutunci da dukiyoyin dukkanin ‘yan Najeriya.
Kasancewar Bello Muhammad Matawalle Dan jihar Zamfara, ya zama wajibi ya taimaka, ya bayar da hadin kai, ya bayar da tallafi da dukkanin goyon bayan da ake bukata, wurin ganin cewa an kawo karshen wannan bala’i da yake faruwa.
A Najeriya Dan Adam ya zama kamar dabba, ana cinikinsa kamar yadda ake cinikin dabbobi! Yawancin kauyuka da garuruwa a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, Sokoto da sauransu duk sun zama kufai!
Kasuwanci a wadannan jihohi da noma da kiwo da sauran ayukkan da bayin Allah suke yi domin su samu abun da zasu ci duk ya mutu kuma ya rushe, ya lalace!
A kashe mutane, ayi garkuwa da su, ayi wa matansu da ‘ya ‘yansu fyade, a hana su ‘yancinsu da walwalarsu kiri-kiri a wannan kasa ta mu?
Haba shugabannin mu, don girma Allah ku ajiye duk wata maganar siyasa. Don girman Allah ku ajiye duk wani banbancin jam’iyyah. Don girman Allah ku manta da duk wata damuwa da ke tsakaninku, ku manta da duk wani banbance-banbance, ku hada hannu, domin ku ceto al’ummarku.
Wallahi, ko shakka babu, al’ummominku suna cikin damuwa, suna cikin matsala da tashin hankali. Yanzu don Allah me zaku fada wa Allah? Wane uzuri zaku kare kan ku da shi a gaban Allah, idan kuka kasa hada kai ku ceto al’ummominku?
Ku sani, wallahi babu ruwan Allah da jam’iyyun siyasar ku. Babu ruwan Allah da banbance-banbancen da ke tsakaninku. Amma ku sani, dukkanin ku Allah Subhanahu wa Ta’ala zai tambaye ku a kan wadannan matsayi da ya baku!
Jihar Zamfara tana cikin tasku da tashin hankali. Bayin Allah Zamfarawa suna ganin bala’i iri-iri, nau’i-nau’i, don Allah me zai hana ku taimaka masu?
Mai girma Gwamna Dauda Lawal, Mai girma Minista Muhammad Bello Matawalle, ku ji tsoron Allah, ku sani zaku mutu ku koma ga Allah. Don haka kuyi tanadin me zaku fadawa Allah, na kin hada kai ku ceto jihar Zamfara daga halin da take ciki.
Eh, tabbas, Allah zai tambayi Shugaba Tinubu a kan halin da jihar Zamfara ta ke ciki, kuma ko shakka babu, Allah zai tambayi mai girma minista Alhaji Badaru; sannan Allah zai tambayi mai girma Nuhu Ribadu; Allah zai tambayi dukkanin jami’an tsaron Najeriya, da duk wani mutum mai ruwa-da-tsaki a kan harkar tsaron Najeriya, amma ku sani, ku ta ku tambayar, wallahi ta musamman Allah zai yi maku, kasancewar ku kun fito daga jihar Zamfara.
A yau ‘yan ta’adda har zasu iya shigowa cikin garin Gusau, anguwar Bulunku da Tsunami, suna daukar mutane, suna shiga da su daji???
Haba mai girma Gwamna Dauda Lawal, haba mai girma minista, Muhammad Bello Matawalle!!!
A gaskiya ya zama wajibi ku sake tsari, ku sake lale, ku sake tunani, ku yaki shaidan, ku ajiye wannan irin banbancin siyasa da ke tsakaninku, ku taimakawa jihar ku ta Zamfara domin Allah.
Don Allah, don Allah, don Allah, ina kira da ku yaki Shaidan da shedanun da suke zuga ku. Don Allah kuyi kokari ku kauda duk wata damuwa da ke tsakaninku. Ku sani, jihar ku ta kama da wuta, ku sani, jihar ku tana cikin matsala da tashin hankali. Ku taimaka, ku ajiye siyasa a yanzu, idan lokacin siyasar yazo sai ayi siyasar.
Kuma ku sani, idan Allah Subhanahu wa Ta’ala ya taimaka, jihar Zamfara ta samu zaman lafiya to ku ne. Haka idan ba’a ci nasara ba (Allah ya kiyaye, amin), to dukkaninku laifin ku ne.
Zamfarawa ba zasu ga laifin mutum guda daga cikin ku, su kyale mutum guda ba.
Domin shi dai mai girma Gwamna Dauda Lawal Allah ya mallaka masa jihar Zamfara, jiha tana hannusa. Shi kuma mai girma minista Alhaji Muhammad Bello Matawalle, yana da sama. Kuma a nan, duk mai hankali yasan me nike nufi. Don haka kenan idan anci nasara duka taku ce, idan kuma an samu akasin haka, to shi ma dukkanin ku ne keda laifi
Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya taimaka maku, ya dafa maku, ya baku ikon hada kai domin taimakon jihar Zamfara da ma Najeriya baki daya, amin.
Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kawo muna karshen wannan bala’i da wannan tashin hankali na rashin tsaro da ya addabe mu, ya bamu lafiya da zaman lafiya a jihar mu da sauran jihohi da ma Najeriya baki daya, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga nan Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post