Tsohon ɗan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore, ya kalubalanci shugaba Bola Tinubu da ya halarci gasar tseren duniya ta ECOWAS da za a yi ranar Asabar a babban birnin tarayya.
Sowore ya yi wannan kira ne a lokacin da ya barbi kayan gudu da zai saka a ranar wannan gudu.
Ya yaba wa ECOWAS bisa wannan kokari na kirkiro irin wannan gudu domin motsa jiki da hakan ke da matukar kyau don lafiyar mutane.
Sai dai kuma a lokacin da ya ke magana ya ƙalubalanci shugaban kasa Tinubu da ya fito a yi wannan gudu da shi.
” Ya kamata shugabanni su rika fitowa ana fafatawa da du a irin haka. Kuma ina kira ga shugaba Tinubu ya fito shima tare da dubban ƴan Najeriya a yi wannan gudu da shi
” Bai kamata a ce za a yi irin wannan gudu na ECOWAS a Najeriya, babu shugaban kasa ba. Shugaban kasa shine shugaba ECOWAS. Kyan shi dai ace shine zai jagoranci wannan gudu da za a yi
Discussion about this post