Kotu a jihar Neja ta yanke wa wani magidanci mai suna Stephen Jiya hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin babbake mahaifiyar sa.
Alkalin kotun Halima Abdulmalik a ranar Alhamis ta ce ta yanke wannan hukunci ne bayan da fannin da suka shigar da kara sun gabatar da shaidu da hujjojin da suka tabbatar wa kotun cewa Stephen ya aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa.
Halima ta ce ofishin Atoni-janar na ma’aikatar shari’a ta jihar ta kama Stephen bayan ya kashe mahaifiyarsa Comfort Jiya tsohuwar ma’aikaciyar ma’aikatar ilimi a watan Disambar 2021.
Ta ce an kama Stephen a ranar 14 ga Satumbar 2022 sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu ranar 23 ga Nuwamba 2022.
A watan Janairun 2022 bayan ya shiga hannun jami’an tsaro Stephen ya tabbatar cewa shine ya kashe mahaifiyarsa.
Stephen ya ce ya babbake mahaifiyarsa saboda yana zargin cewa tana da hannu a Korar matarsa daga gidansu dake Suleja.
Discussion about this post