Kwamitin Karɓar Koke-koke na Majalisar Tarayya, ya bada sammacin kamo Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, saboda ƙin amsa gayyatar bayyana a gaban kwamitin da ya yi, domin amsa wasu tambayoyin da suka shafi harkar fetur.
Haka kuma kwamitin ya bada wani sammacin na neman a kamo Akanta Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein da kuma wasu shugabannin kamfanonin fetur su 17.
Daga cikin shugabannin kamfanonin fetur ɗin da za’a kamo, akwai Shugaban Kula da Hada-hadar Zuba Jari, NAPIMS, akwai na Ethiop Eastern Exploration and Production Company Ltd, da kuma na West Africa Exploration and Production.
Bada sammacin kamo su ya biyo bayan shawarar da ɗan kwamitin mai suna Fidelis Uzowanem ya gabatar a zaman kwamitin na ranar Talata.
Shugaban Kwamiti, Micheal Etaba, ɗan APC daga Cross River, ya ce Cardoso da sauran duk sun yi biris da gayyatar da kwamiti ya yi masu.
Ganin haka ne sai wani mamba a kwamiti mai sun Fred Agbedi, ɗan PDP daga Bayelsa, ya amince aika masu sammacin kamu, kuma sauran ‘yan kwamitin duk su ka amince da kamo su ɗin.Agbedi ya ce ana buƙatar ana so waɗanda ake gayyatar su tabbatar sun bayyana a gaban kwamiti a ranar 14 g Disamba.
Kwamitin ya bada odar sammacin ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun cewa ya cika aikin kamo waɗanda suka bijire wa gayyatar da Majlisa ta yi masu.
Rashin fahimtar dai ta samo asali ne tun daga wani ƙorafi a wani mai suna Uzowanem ya shaida wa Majlisa ƙorafin sa kan rahoton da NEITI ta fitar a 2021.
Ya ce ƙungiyar NEITI ta gano yadda ake cuwa-cuwa da danƙara harƙalla a tsakanin kamfanonin mai da manyan jami’an gwamnati.
“Kuɗaɗen Kasafin 2024 har Naira tiriliyan 27.5, to idan aka yi amfani da rahoton NEITI za a iya ƙwato kuɗaɗen da suka kai adadin kasafin na Naira tiriliyan 27.5.” inji shi
Ya yi bayanai dangane da yadda wasu manyan kamfanonin fetur na waje ke satar miliyoyin daloli na NNPC.
“NNPCL sun wawuri dala miliyan 124 ta hanyar kamfanin TOTAL, amma an yi shiru babu zancen kuɗaɗen.
“Kamfanin Chevron ya karkatar da dala miliyan 76. Amma maganar gaskiya dala miliyan 267 ce aka danƙara masu.
“An karkatar da wata dala miliyan 190 ta hannun Chevron, sai dala miliyan 188 ta hannun Agip. Amma NEITI bai bayyana waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba.”
Discussion about this post