Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gargadi mahukuntan Isra’ila da kada su bi ‘yan kungiyar Hamas a yankin Turkiyya.
“Idan suka kuskura su dauki irin wannan matakin kan Turkiyya, to za su dandana kudar su ta yadda ba za su iya farfadowa ba har abada,” in ji Erdoğan a lokacin da ya dawo daga Qatar a ranar Laraba.
Bayanin na Erdoğan ya fito ne daga ofishin sadarwarsa da ke amsa tambaya kan shirin hukumar leken asirin kasar Isra’ila na kashe ‘yan kungiyar Hamas a kasashen waje.
Tun da farko a ranar Litinin, kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ambato hukumomin leken asirin Turkiyya na cewa Isra’ila za ta fuskanci “mummunan sakamako” idan ta kai hari kan ‘yan Hamas a Turkiyya.
Jaridar Wall Street Journal a baya ta bayar da rahoton cewa ma’aikatan sirri na Isra’ila suna shirin bin kasashen da domin kashe shugabannin Hamas a duniya bayan kawo karshen yakin Gaza.
Turkiyya na da alaka da kungiyar Hamas mai kishin Islama ta Falasdinu, ta kuma yi watsi da sanya kungiyar a matsayin ‘yan ta’adda, wanda kasashen Turai da Amurka ke yi.
Discussion about this post