Kamar yadda ya zaman to al’ada ga dukkanin sabbin gwamnatoci, su tantance ma’aikatan da suka gada. Bisa dalliln tantance ma’aikatan gaskiya da kuma na bogi.
Wasu lokutan bisa zargin yin almundahana a kan biyan albashi ko karin girman bogi.
A wannan zangon ma, Gwamnatin Jihar Jigawa karkashin jagoracin Malam Umar Namadi tana shirin kammala tantance ma’aikatan jahar.
Abu ne mai kyau dan sanin makamar aiki da kuma shinfida ka’ida mussamman waje kuddiga da yadda a ke kashe kudin al’ummah a kan gaskiya, yin wannn tantancewa ta ma’aikata za ta taimakaw gwamnatin wajen tsare tsaren ta da dama.
Sai dai, kash! Sabanin yadda irin wannan aiki ya ke kasancewa ya sha banban da makamancin sa na baya, bisa wasu dalilai da muka hankalta da su, kamar haka.
Na farko, lokacin da tsarin da aka yiwa aikin tantance ma’aikatan ya gamu da cikas, hatta a wurin tantancewar a kwai hargowa da kin bin ka’ida.
Na biyu, ma’aikatan da ke wajen babban birnin Jaha, musamman malam makarantu ba a yi musu wannan tantancewar ba, duk da an sanya lokaci da ranakun da za a je kowace ma’aika don yin wannan aiki.
Na uku, zargin karbar na goro da ga wurin ma’aikatan da za tantance su ya yi yawa, cin hanci da rashawa ya shiga ciki aikin dumu, dumu, kamar yadda wasu ma’aikatun sai sun tara makudan kudade sun bawa masu wannan aiki, kafin a tantance su, wasu ma’aikatan na bada hanci kama da dubu daya zuwa biyar, don kawai a tantance su.
A bin mamaki a nan, wannan masu aikin, kamar wani kamfani ne a ka bashi kwantiragin yin wannan aiki.
In har wannan zargi ya tabbata gaskiya, ya kamata, Maigirma Gwamna ya dau mataki a kai, mussan imanin ‘Yan Jigawa a kan gaskiya da rikon amanar Malam, mussamman a kan abin da ya shafi hakkin talaka.
Abu na hudu, sanarwar da aka samu da ga Ma’aikatar kudi ta jahar jigawa, na bada lokaci na karshe, domin kowane ma’aikaci ya tabbatar yaje an tantance shi a Birnin Dutse, ko ya dauki kansa a matsayin ba ma’aikaci ba, ya jawo cece kuce a wurin al’umar Jihar Jigawa.
Yanayin albashi da talaucin da al’ummah suke ciki, ba karamin tsanani za a saka su ba, in har a kace, sai sunje Dutse don a tantance su, kuma a cikin karamin lokacin da a ka sanya domin yin aikin.
Yawan mutanen nan da ba a tantance su ba, ba laifin su bane, domin masu aikin ne basu je sun same su ba kamar yadda a ka tsara ba.
Da fatan, Maigirma Gwamna zai lura da wannan tsokaci.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post