Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje yayin da yake jawabi ga ya’yan Jam’iyyar APC na jihar Kano da Kasa baki daya ya bayyana cewa likimo suka yi suka zura wa jagorar kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso Ido kawai yana ta karakainarsa na takarar shugaban kasa da kuma ganin dole dan takararsa Abba Yusuf ya yi nasara a zaben Kano.
Ganduje ya ce ” Tun da muka ga abinda ya fi maida hankali a akai shine ya zama shugaban kasa sannan Abba ya zama gwamna, ya manta cewa dan takararsa ba sunan sa a cikin rajistar zaben jam’iyyar da yake takarar akai wacce ke a hukumar zabe ta kasa, sai muka yi likimo muka zura mai ido kawai.
” Jam’iyyar mu a Kano sai muka ja baki muka yi shiru, muka barshi da makarraban sa suna ta cika baki, ba su san muna da takubban yakin mu washe ba. Muna jiran ranar daukan fansa ne kawai.
Nation ta wallafa cewa, bayan haka Ganduje ya ce suna da yakinin ko a Kotun Koli, APC ce za ta yi nasara a shari’ar.
Zan je Kotun Koli – Abba Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya bayyana aniyar sa ta garzayawa Kotun Ƙoli, domin sake ƙalubalantar tsige shi da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe ta Abuja ta yi a ranar Juma’a.
“Ina sanar da al’ummar Jihar Kano da sauran ‘yan Najeriya cewa, bisa matsayar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar mu suka cimma, mun umarci lauyoyin musu gaggauta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.
“Mu na da yaƙinin cewa a Kotun Ƙoli a a yi mana adalci, ta hanyar jingine rashin adalcin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta yi mana a Kano.
“Muna kuma da yaƙinin cewa Kotun Ƙoli za ta tabbatar mana da zaɓen mu da al’ummar Jihar Kano su ka yi.” Haka gwamnan ya tabbatar, a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna ɗin, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar.
Yusuf ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Kano su ci gaba da gudanar da harkokin su, yayin da gwamnati ta ɗauki matakan da suka wajaba, domin tsare dukiyoyi da rayukan jama’a.
Ya tabbatar da cewa ɗan tsaikon da aka samu ba zai sare wa gwamnatin guiwa ba, wajen ci gaba da ƙoƙarin da ta ke yi domin gina ayyukan raya jiha da inganta rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya.
Maimakon haka, Abba ya ce zai ci gaba da bijiro da ayyukan more mulkin dimokraɗiyya ga al’ummar jihar Kano.
Daga nan ya yi kira da ‘yan jiha da ƙasa baki ɗaya su ci gaba da yi wa Jihar Kano addu’a, domin Allah ya kuɓutar da ita daga rashin adalcin da aka yi wa jihar.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa Gwamna Abba bai cancanci zama gwamna ba, domin a cewar ta, a lokacin da aka yi zaɓe, shi ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne.
Kotun bisa jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ta ce wasu adadin ƙuri’un da aka dangwala wa Abba a lokacin zaɓe, ba su da tambarin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Discussion about this post