Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Bara Ka Tuh
Dukkanin kyakkyawan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah Madaukaki, taimakonsa da gafararsa muke nema; kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar to babu mai shiryar da shi.
Kuma lallai ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya. Kuma lallai ina shaida cewa, Annabi Muhammad (SAW) bawansa ne kuma manzonsa ne.
Bayan haka, ya ku ‘yan uwana, masoyana, masu daraja, masu girma, masu albarka! Maganarmu ta yau ta shafi daya daga cikin rukunnan imani guda shida, wanda duk wanda bai yi imani da shi ba, ko kuma yayi musu a kansa, to Allah ba zai karbi ayyukansa ba, ba zai taimakeshi ba, kuma ba zai bashi nasara a rayuwarsa ba. Wannan kuwa shine bayar da gaskiya tare da yin imani da yarda da amincewa da kaddarar Allah, tare da imani, da yarda da abunda ya hukunta.
Yin imani da kaddarar Allah rukuni ne mai girma, wanda ta hanyarsa mutum yake samun natsuwa a rayuwarsa, sannan kuma ya samu amsoshi gamsassu, kuma cikakku dangane da abubuwa masu yawa, wadanda suka shige masa duhu a wannan rayuwa mai cike da kalubale da hadurra daban-daban. Allah Madaukaki yana cewa:
“إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَر.”
“Hakika Mun halicci komai a bisa kaddara.”
Kuma Allah Madaukaki yana cewa:
“الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّى. وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَى.”
“Shine (Allah) wanda yayi halitta, kuma ya daidaita ta, kuma shine wanda ya kaddara abubuwa, kuma ya shiryar da su.”
Kuma Allah Madaukaki yana cewa:
“وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا.”
“Kuma ya halicci kowane abu, kuma ya kaddara shi kaddarawa.”
Ya ku bayin Allah masu daraja! A takaice dai ayoyin da suke tabbatar da wannan muhimmin rukuni na imani da kaddarar Allah da hukuncinsa, sun fi a kirga.
Sannan a cikin Sunnar Manzon Allah (SAW), a wurare daban-daban, masu yawa, Annabi ya tabbatar da wannan rukuni mai girma na yin imani da kaddarar Allah. Misali, a cikin Hadisin da mala’ika Jibrilu (AS) yazo wurin Annabi (SAW), yana tambayarsa, da ya tambaye shi akan imani, sai yace:
“Imani shine, ka bayar da gaskiya da Allah, da mala’ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar karshe, da yarda da kaddara, mai dadi da marar dadi.” Sai Jibrilu yace, “Kayi gaskiya!” [Muslim ne ya ruwaito shi]
Ya ku ‘yan uwa masu daraja! Abin da ake nufi da kaddara, shine, ilimin Allah Ta’ala wanda ya rigaya tun fil-azal, a kan abubuwa kafin su auku, kuma Allah ya rubuta su daki-daki kafin ya halicci sama da kasa da shekara dubu hamsin, kuma sannan babu wani abun da zai auku, ko menene, face da saninsa kuma da ganin damarsa, kuma shi ya halicce shi. Wannan shine bayar da gaskiya da kaddara a wurin Annabi (SAW) da Sahabbai, kuma shine bayar da gaskiya a wurin Ahlus-Sunnah wal Jama’ah.
Don haka, tilas ne ga duk wani Musulmi, wanda ya amsa sunansa na Musulunci, ya yarda cewa babu wani abu da zai faru cikin mulkin Allah, wanda sai daga baya Allah zai san shi. A’a, Allah ya rigaya, yasan komai tun fil-azal, kuma ya rubuta shi a allon kaddara, wanda yake wurinsa (wato lauhil mahfuz), kamar yadda yazo a cikin ingantaccen Hadisi, kuma kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:
“إِنَّ ذَلِكَ فِي كِتَابٍ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ.”
“Lallai hakan, yana cikin littafi, lallai hakan mai sauki ne a wurin Allah.”
Don haka mu sani, babu wani abu da zai auku, ko zai faru, face sai Allah ya sani, kuma ya ga dama. Kuma idan zai auku, zai auku ne kamar yadda Allah ya tsara kuma ya zartar. Allah Madaukaki yana cewa:
“وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا. يُدْخِلُ مَنْ يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا.”
“Ba za ku yi nufin aikata wani abu ba, face sai Allah yayi nufi. Lallai Allah masani ne, mai hikima, yana shigar da wanda yayi nufi cikin rahamarsa, kuma azzalumai yayi masu tanadin azaba mai girma.”
Ya ku ‘yan uwana! Ku sani, babu tilas ga dan Adam akan ayyukansa, a cikin akida ta Musulunci. Kuma mutum yana da dama da kuma zabi, ya aikata abin da ya ga dama, kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:
“وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ.”
“Kuma mun shiryar da shi hanyoyi biyu (wato na alkhairi da na sharri).”
Don haka, idan mutum ya zabi ya bi hanyar alkhairi a wannan rayuwa don kan sa. Idan kuma ya zabi yabi hanyar sharri don kansa.
Bayin Allah masu girma! Wadannan sune matakan kaddara guda hudu kamar haka:
1. Allah ya san komai: Ya san abin da ya faru da abin yake faruwa, da wanda zai faru nan gaba, da kuma idan zai faru ta yaya zai faru.
2. Allah ya rubuta komai da zai faru har zuwa tashin al-kiyama.
Kuma yazo a cikin Sunnah, a cikin Hadisin Abdullahi dan Amr Dan Ass, Manzo Allah (SAW) yace:
“Allah ya rubuta abubuwan da ya kaddarawa halitta kafin ya halitta sammai da kasa da shekara dubu hamsin.”
3. Sai Allah yaso faruwar abu sannan zai faru, domin duk abin da Allah yaso wakanarsa zai wakana, abin da bai ga damar wakanarsa ba ba zai wakana ba.
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Hurairah (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace:
“Ka da dayanku yace, Ya Allah ka gafarta mani in ka ga dama. Ya Allah ka jikaina in ka ga dama. Mutum yayi da gaske cikin addu’arsa, domin shi Allah yana aikata abin da ya ga dama ne, babu mai tilasta shi.”
4. Halittar Allah ga abubuwa, da samar da su da kudurarsa cikakkiya. Allah shine ya halicci kowane mai aiki da duk aikinsa, da duk wani mai motsi da motsinsa, da duk wani mai sukuni da sukuninsa.
Bukhari ya ruwaito daga Imran Bin Husaini, daga Annabi (SAW) yace:
“Allah yana nan, lokacin da babu wani abu tare da shi. Kuma al’arshinsa ya kasance a kan ruwa. Kuma ya rubuta komai a cikn lauhul mahfuz. Kuma ya halicci sammai da kasa.”
Don haka dole ne Musulmi yayi imani da wadannan matakai na kaddara guda hudu. Kuma duk wanda ya musanta daya daga cikinsu to bai yi imani da kaddara ba baki daya.
Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa, Imani da kaddarar Allah yana da fa’idoji, wadanda sune kamar haka:
1. Cikakken dogaro ga Allah, lokacin da bawa yabi matakan da ya kamata ya dauka na sababi da addu’a da rokon Allah. Domin Allah shine wanda yake halittar sababi, da abin da sababin yake haifarwa.
2. Samun natsuwar zuciya. Saboda bawa ya san cewa, duk abin da ya faru kaddara ce daga Ubangiji.
3. Rashin jiji-da-kai lokacin da bawa zai samu muradinsa. Domin haka kaddara ce daga Allah, domin shine ya hore masa hanyoyin samun alheri. Don haka sai ya godewa Allah, ya gujewa jiji-da-kai.
4. Rabuwa da damuwa da bacin rai, a lokacin da bawa ya rasa samun abin da yayi muradi, ko yake son cimmawa. Domin hakan ya faru ne da kaddarar Allah da hukuncinsa. Don haka sai yayi hakuri, Allah zai ba shi lada a kan hakan, kuma da ikon Allah, sanadiyyar hakurin da yayi, da imanin da yayi da kaddara, Allah zai biya masa dukkanin bukatunsa daga karshe, kuma Allah zai dora shi akan nasara.
Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Ya kai dan Adam! Ka sani, da al’ummah baki daya za su taru, domin su cutar da kai da wani abu, to ba za su iya ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka. Haka ma, da za su taru don su amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanarka ba, sai da abin da Allah ya rubuta.”
Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Idan wani abu ya same ka, kada ka ce ina ma na yi kaza, ko kaza, a’a, ka ce, kaddara ce ta Allah, kuma abin da ya ga dama shi zai aikata. Domin ‘da’ tana bude kofar shaidan.”
Haka kuma ya tabbata a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW) yace:
“Abin mamaki ga lamarin mumini: Idan abin dadi da farin ciki ya same shi, sai ya gode wa Allah, hakan sai ya zamo masa alkhairi; haka nan idan wata cuta ko wata damuwa suka same shi, sai yayi hakuri, hakan sai ya zame masa alkhairi.”
Kuma Ali ya rawaito cewa, Manzon Allah (SAW) wata rana ya na wurin jana’izah, sai ya dauki wani abu, yana tona kasa da shi. Sai yace, “Babu wani mutum, face an rubuta mazauninsa na wuta ko na Aljannah.” Sai suka ce, “Ya Ma’aikin Allah! Ba za mu dogara da abin da aka rubuta muna ba, mu daina aiki?” Sai yace, “A’a! Ku yi aiki. Domin kowa za a sawwake masa abin da aka halicce shi don shi. Wanda ya zamo mai rabo, sai a sawwake shi a cikin aikin masu rabo, haka wanda yake cikin tababbu, sai a sawwake shi a cikin aikin tababbu.”
Sannan kuma lallai Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW):
عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال:
“إن عِظَمَ الجزاءِ مع عِظَمِ البلاءِ، وإن الله تعالى إذا أحب قوما ابتلاهم، فمن رَضِيَ فله الرِضا، ومن سَخِطَ فله السُّخْطُ.” [صحيح – رواه الترمذي وابن ماجه]
Daga Anas Dan Malik – Allah ya yarda da shi – yace Annabi (SAW) yace:
“Lallai gwaggwabar lada mai yawa mai tsoka tana tare da girman bala’i da jarabawa, kuma Allah Mai girma da daukaka idan yana son wasu mutane to sai ya jarrabesu; duk wanda ya yarda da jarrabawar Allah, to sai ya sami yardar Allah da nasararsa, kuma duk wanda yayi fushi da kaddarar Allah, to shi ma sai Allah yayi fushi da shi.” [Hadisi ne ingantacce, Ibnu Majah ne ya Rawaito shi, haka Al-Tirmizi ma ya Rawaito shi]
Bayin Allah masu albarka! Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bamu labari a cikin wannan Hadisi cewa, mumini a wasu lokutta, wani abu na musibu da jarabawa su kan same shi; sukan same shi a kan sa, ko a dukiyarsa, ko a kan mulkinsa, ko a kan iyalinsa ko waninsa; kuma Allah zai bashi lada akan kowace musiba da jarabawa da ta same shi; sannan Annabi (SAW) ya bayyana cewa musibu ko jarabawa, a koda yaushe suka zamo manya, kuma hadarin su ya girmama, to ladansu yakan girmama a wurin Allah. Sannan Annabi (SAW) yayi bayanin cewa afkuwar musibu da jarabawar Allah yana daga cikin alamomin son Allah ga mumini. Kuma hukuncin Allah da kaddararsa babu makawa sai sun afku, sai dai kuma wanda yayi hakuri kuma ya yarda da kaddarar, to Allah zai saka masa kan hakan da yardarsa, kuma babu ladan da yafi wannan. Kuma duk wanda yayi fushi kuma yaki yarda da kaddarar Allah, to Allah zai yi fushi da shi, kuma babu ukubar da tafi wannan.
Sannan ya kamata al’ummar Musulmi mu sani, hakuri da yarda da kaddarar Allah da hukuncinsa, baya kore mutum yabi kadin hakkinsa, musamman wanda azzalumai suke kokarin danne masa. Sannan hakuri da yarda da kaddarar Allah da hukuncinsa, baya nufin kar bawa yabi wani sababi daga cikin sabubban da shari’ah ta amince muna mu bi domin mu samu biyan bukata daga wurin Allah Madaukaki.
Sannan kuma mu sani, kamar yadda muka yi imani da kaddarar Allah da hukuncinsa, haka kuma dole muyi imani cewa, ita addu’a tana canza kaddara.
To idan duk muka san wannan, zamu samu natsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarmu baki daya. Sannan kuma babu wani abun da zai tayar muna da hankali, komai gurmansa, kuma ko mai hadarinsa.
Sannan daga karshe, su kuma azzalumai a duk inda suke, a ko’ina suke a fadin duniyar nan, su sani, wallahi duk abunda suke yi Allah yana sane, kuma yana kallonsu. Kuma duk abunda suke yi, kar suyi tsammanin Allah ya kyale su ne, a’a, ba haka bane. Allah ya bar su ne, yana yi masu istidraji ne, wato daurin talala mai kamar sake. Don haka, a duk lokacin da zai kama su, a duk lokacin da zai damke su, wallahi su sani, kamun Allah da damkarsa bana wasa bane, kuma babu sauki a cikinsa.
Don haka, idan sun ji tsoron Allah, suka daina abunda suke yi na zalunci, sai Allah ya taimakesu, kuma ya yafe masu zunubansu. Idan kuma sun ci gaba, to su sani, GA SU GA ALLAH…!
Shi kuma wanda ake zalunta, ko wanda aka zalunta, mu sani, Allah yayi alkawarin zai taimake shi, ko mai tsawon lokaci. Don haka muje zuwa…!
Allah yasa mu dace, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post