• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    court

    Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    ‘Yan sanda sun kama wani da ya shahara wajen yi wa mutane damfara ta Facebook

    #EndSARS: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan zargin kisan masu zanga-zanga a Lekki, Lagos

    Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

    Abuja bill-board

    RASHIN TSARO – Abuja ta zama matattarar batagari da masu sace mutane – Dan majalisa

    NYSC

    Za a yi wa shirin yi wa kasa hidima, NYSC, garambawul – Gwamnati

    Gwamnatin Tinubu ba za ta ƙaƙaba wa jama’a takunkumin hana magana ba – Minista

    SHIRIN WAYAR DA KAI: Ministan Yaɗa Labarai ya kafa kwamitin tsara daftarin cusa ɗa’a, kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u

    KISAN MASU MAULIDI: Mun samu gawarwaki 85 – Hukumar Agajin Gaggawa

    KISAN MASU MAULIDI 85: Sarkin Musulmi, Shehunan Tijjaniya, Dattawan Arewa da Shugaban Izala sun ce ba za a yafe ba

    TARON COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Najeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba – Minista Idris

    TARON COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Najeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba – Minista Idris

    Uba Sani ya yi alhini da ta’aziyyar kisan dandazon ƴan maulidi a Kaduna, ya umarci a gudanar da bincike

    Uba Sani ya yi alhini da ta’aziyyar kisan dandazon ƴan maulidi a Kaduna, ya umarci a gudanar da bincike

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Saura ƙiris Liverpool ta zubda abin faɗi a wasan Premier League na ranar Lahadi

    Saura ƙiris Liverpool ta zubda abin faɗi a wasan Premier League na ranar Lahadi

    MESSIN DAI: Leo Messi ya lashe kyautar ɗan kwallon duniya ta Ballon d’Or a karo na takwas

    MESSIN DAI: Leo Messi ya lashe kyautar ɗan kwallon duniya ta Ballon d’Or a karo na takwas

    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Dalilin da ya sa na ziyarci Tinubu – Uba Sani

    BIDIYO: Dalilin da ya sa na ziyarci Tinubu – Uba Sani

    BIDIYO: Tinubu masoyin ‘Yan jarida ne – Idris

    BIDIYO: Tinubu masoyin ‘Yan jarida ne – Idris

    Timipre-Sylva

    TANGARƊA A APC: Kotu ta hana Sylva, tsohon Ministan Fetur tsayawa takarar zaɓen gwamnan Bayelsa

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

No Result
View All Result

Soki-Burutsun Bello Matawalle Da Sunan Hira, Daga Imam Murtadha Muhammad Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
November 9, 2023
in Ra'ayi
0
Dole A Dakatar da Kashe Ƴan Arewa a Kudu -Gwamna Matawalle

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu alaikum

Yaku bayin Allah! Ku sani, tabbas, hakika, ana iya gane nagartaccen shugaba ne, jarumi, jajirtacce, mai ilimi, mai basirah da hangen nesa, da kishin al’ummah ta hanyar maganganunsa da mu’amalolinsa sa kuma irin yadda yake jagorantar al’ummarsa.

Game da soki-burutsun da tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi da sunan wai fira, ai a wannan shirme nasa, babu abunda al’ummar jihar Zamfara zasu ce illa, idan mai magana wawa ne, to masu sauraro ba wawaye ne ba.

Ikon Allah! Wai irin wadannan mutane, sune Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jarrabi jihar Zamfara da su a matsayin shugabanni a can baya. To irin wadannan don Allah ta yaya zasu iya gabatar da wani abun azo a gani ga al’ummar da suke jagoranci?

Kuma mu abunda ya kamata al’ummah su gane, kuma su fahimta shine: jihar Zamfara ita ce farko ga dukkanin wani mutum dan jihar kuma mai kishin jihar. Babu ruwan mu da wani mutum, ko ace wai mutum muke kallo ko kiyayya da wani mutum. Sam ba haka bane. Mu dai jihar mu ta Zamfara kawai.

Kuma wajibi ne mu sani, Zamfarawa mutane ne masu hankali, masu ilimi, masu basirah, hakuri, juriya da hangen nesa. Su ba jahilai bane kawai da wani zai zauna a gaban kyamara da bututun magana, ya fadi maganganu iya son ran sa, kuma kawai su bishi, ido rufe cikin jahilci, su yarda da abun da ya fada na shirme da soki-burutsu.

Mu a jihar Zamfara, dukkan wani mutum, wanda yayi wata fira ko wasu jawabai, to sai mun auna wadannan maganganu da kalamai nasa, mu dora su akan sikeli na ilimi, tare da dubon hujjojin da mai maganganun ya kawo.

Idan maganganu ne da suke kan hanya to zamu dauka, muyi aiki da su, ba tare da kallo, ko dubo, ko la’akari da wanda yayi maganganun ba.

Idan akwai kanshin gaskiya cikinsu zamu dauke su, kuma mu yarda, kuma muyi aiki da su. Amma idan shirme ne, soki burutsu ne, shiririta ne, to gaskiyar magana, wallahi zamu yi watsi da su, mu dauke su banza da shirme. Mu dauke su irin maganganu na teburin mai shayi.

Sannan kuma mu Zamfarawa babu ruwan mu da jam’iyyar mutum ko kuma wa yake goyon baya. Kawai duk Gwamnan da yazo muna auna shi ne da irin alkhairi ko ci gaba ko ayukkan da yayi wa Zamfarawa. Ba muna soyayya ko adawa ido rufe bane, kuma wallahi babu wani mutum, ko shi wanene, da muke yiwa makauniyar soyayya, don kudinsa, ko mulkinsa, ko jam’iyyarsa, ko matsayinsa. A’a, mu tambayar mu ita ce, ME KA YIWA JIHAR ZAMFARA DA ZAMFARAWA? Kawai wannan shine magana.

Na kalli firar da Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal yayi, haka kuma na kalli firar da tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle shi ma yayi.

Wallahi duk wanda ya natsu, kuma yayi hukunci tsakaninsa da Allah akan jawaban kowa daga cikinsu, to zai gane cewa, jawaban Gwamna Dauda Lawal sune aka yi bisa ilimi da basirah; kuma sune suke kan hanya. Amma jawaban tsohon Gwamna Matawalle kawai ba komai bane illa shirme da soki-burutsu da shiririta.

Asalin maganar fa ita ce, zarginsa Gwamna Dauda Lawal yake yi, kuma wannan zargi ba gwamna kawai ne yake yi masa su ba, a’a, wallahi zargi ne na dukkanin al’ummar jihar Zamfara, da suke yiwa Bello Matawalle.

Ya kamata Bello Matawalle ya sani, kafatanin Zamfarawa suna zarginsa da ya kashe jihar Zamfara, ya cuci al’ummar jihar Zamfara, ya mayar da jihar baya ta ko wane bangare. Don haka, mu har gobe, muna binsa bashin kare kansa daga wadannan zarge-zarge da muke yi masa, mu ba wai bukatar muke yi ya fito ya cika mu da maganganun banza, na shirme da soki-burutsu ba.

Shin Bello Matawalle ko kana nufin ka dauke hankulan mu da maganganun shirme, marasa tushe balle makama, domin mu mance da zage-zagen da muke yi maka? To idan haka ne, ka sani, wallahi baka yi nasara ba, kuma ka makara, kuma kayi latti. Domin wallahi, Allah ya sani, mu kar muke kallon ka. KIFI NA GANIN KA MAI JAR KOMA!

Ka sani Bello Matawalle, kai ma da kazo kan gadon mulkin jihar Zamfara, munyi maka irin wannan kyakkyawar fata da addu’o’in da muke yiwa Gwamna Dauda Lawal, amma sai ka barar da garin ka, ka lalace, ka biye wa wasu ‘yan siyasa, marasa kishin jihar mu da al’ummar mu. Ka shiga sharholiya da almubazzaranci fa dukiyar al’ummah. Ganin haka yasa muka janye goyon bayan mu daga gare ka.

To yanzu sai Allah ya kawo Dauda Lawal, muka duba, muka lura da kamun ludayinsa, muka ga cewa lallai wannan mutum yana da kyakkyawar manufa ga jihar Zamfara da al’ummarta, shi yasa shi ma muka bashi goyon baya, muke yi masa addu’o’in samun nasara da fatan alkhairi. Wannan shine kawai.

Saboda haka, daga karshe, Bello Matawalle, ya kamata ka sani, wannan firar taka, wadda kayi da DCL Hausa, ba abunda ta canza, kuma babu abunda zata canza. Kuma har gobe, da ikon Allah, kimar Dauda Lawal tana nan a idanun al’ummar jihar Zamfara.

Domin shi mutum ne mai kima, mai mutunci, mai ilimi, mai basirah, mai hangen nesa, mai son kawo ci gaba, mai son ya gyara jihar mu mai albarka, mai kishin jihar mu da al’ummar jihar baki daya.

Don haka, duk wata karya, da kage, da kazafi, da shirme, da soki-burutsu, ba zasu taba sa al’ummah su daina goyon bayan gwamnatin Dauda Lawal ba. Hasali ma, sai dai wannan ya kara masa farin jini da soyayyar al’ummah.

Mu al’ummar jihar Zamfara mun gaji da irin halin da muke ciki na rashin tsaro da tabarbarewar jihar mu da ci bayan da muke ciki. Mu yanzu wanda zai taimake mu, Allah yayi amfani da shi, ya gyara jihar mu shi muke nema, kuma shi muke yiwa addu’a da rokon Allah da fatan alkhairi.

Yanzu Bello Matawalle don Allah ya dace ace tun da aka yi zabe, ka fadi zabe, Allah ya dora Dauda Lawal, amma baka tafi jihar ka ba, baka san halin da muke ciki ba, babu ruwan ka da matsalolin mu, kawai don Allah bai baka nasara a zabe ba? Laifin me muka yi maka? Mu muke bayar da mulki ba Allah ba?

Tun da fa aka yi zabe ka fadi, ka kwashe dukkanin iyalanka, da duk wasu kayan bukata naka, ka bar jihar Zamfara baki daya, ka koma Abuja, ka tare can. Yanzu wannan don Allah yana nuna kenan kana kaunar jihar Zamfara da al’ummarta? Haba Bello Matawalle, kai ma kasan wallahi dole wannan ya bata wa Zamfarawa rai, kuma dole muce baka son mu, kuma baka kaunar mu. Idan mun fadi haka kuma bamu yi wa kowa laifi ba.

Yanzu don Allah haka ka ga tsohon gwamna, mai girma Alhaji Abdul’aziz Yari yayi? Shin ya gudu ya bar jiharsa da al’ummarsa?

Wallahi shi yasa muke kallon Abdul’aziz Yari a matsayin rikakken dan siyasa, kuma jigo a siyasar jihar Zamfara da Najeriya baki daya. Domin ko yana kan mulki, ko baya kan mulki, sam bai bar jihar Zamfara ba, kuma bai bar al’ummarsa ba. Kuma wallahi dole ne mu jinjina masa akan wannan.

Dukkanin gwamnonin da aka yi a baya, tun lokacin da aka kirkiro jihar mu ta Zamfara; tun daga Kanal Jibril Bala Yakubu, har zuwa Ahmad Sani Yariman Bakura, har zuwa Mamuda Aliyu Shinkafi, har zuwa Abdul’aziz Yari, ko wane daga cikinsu yana iya nuna abunda yayi na ci gaba a jihar Zamfara, duk da cewa, mun san a matsayin su na ‘yan Adam, suna da nasu irin kurakurai, to amma don Allah kai me zaka nuna naci gaba da ka kawo wa jihar Zamfara, a shekaru hudun da kayi kana mulki, in ban da tabarbarewa da ci baya?

Ya kamata fa muji tsoron Allah, mu fada wa kawunanmu gaskiya.

Yanzu misali, a irin halin da jihar Zamfara take ciki na matsanancin rashin tsaro da yunwa da talauci da matsaloli iri-iri, don Allah ya kamata ka koma gefe kana fada da gwamna, a matsayinka na ministan tsaro? Shin ba kamata yayi ka sa hannu, ka taimaka, domin Allah ya taimake mu, ya kawo muna karshen wadannan matsaloli ba. Amma sai Kaki yin hakan, wai kai ka koma Abuja, kana fada da Gwamna, saboda Allah ya karbi mulki daga hannunka ya bashi. To laifin sa ne? Ba Allah ne yake kwace mulki, ya bayar da shi ga wanda yake so ba?

Maimakon kasan cewa Allah ne mai yi, ku hada hannu, ku nemi taimakon Allah, ku taimaki jihar mu, sai ka koma kana wadannan maganganu na shirme, marasa tushe balle makama.

Don haka, Bello Matawalle muna kira da kaji tsoron Allah, ka gyara, domin ci gaban jihar mu ta Zamfara da al’ummarta.

Sannan daga karshe, don Allah ina kira ga dukkanin al’ummar jihar Zamfara, da muci gaba da yiwa Gwamnatin Dauda Lawal addu’o’in Allah ya bashi nasara, kuma tare da yi masa fatan alkhairi.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh

Allah ya kyauta, amin.

Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Zaku iya samun Imam ta wannan lamba kamar haka: 08038289761.

Tags: AbujaDaudaHausaLabaraiMatawalleNewsPREMIUM TIMESTsaroZamfara
Previous Post

RANAR KIMIYYA TA DUNIYA: UNESCO Ta Jaddada Muhimmancin Kimiyya Ga Ci Gaban Duniya

Next Post

Za mu gina Otel Otel bisa ruwa idan na zama gwamna – Dino Melaye

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Za mu gina Otel Otel bisa ruwa idan na zama gwamna – Dino Melaye

Za mu gina Otel Otel bisa ruwa idan na zama gwamna - Dino Melaye

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda farashin magungunan Mura, Zazzabi, da sauransu suka yi tashin gwauron zabi cikin shekaru Hudu a Najeriya
  • DUBU TA CIKA: ‘Yan sandan Adamawa sun cafke wani matashi da ya rika yi wa babbar Zakara fyade yana lalata da wannan Zakara
  • Gwamnati ta fara horas da ma’aikatan lafiya hanyoyin dakile yaduwar cutar diphtheria
  • Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu
  • KISAN TUDUN BIRI: Uba Sani ya zama Uba da Uwa ga ya’yan da suka rasa iyaye a sanadiyyar harin

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.