Shugaban hukumar Zabe ta Kasa, Mahmood Yakubu ya yi kira ga ‘yan siyasan Kogi su wa Allah su hada kai su bari a yi zaben jihar salin- Alin.
Hukumar ta yi wannan roko ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na yini daya a ranar Talata a Lokoja, babban birnin jihar.
Yakubu wanda ya samu wakilcin Kwamishinan zabe da ke kula da Kogi da Kwara, Sani Adamu ya ce burin hukumar shine ta ga an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihar.
“Saboda haka, dole ne ku bi ka’idojin da hukumar ta tsara domin a gudanar da zabe mai ma’ana a jihar. Sannan kuma mu tabbat mun yi abu kamar masu hankali domin samun nasara hakan.
Mu a hukumar zabe a shirye muke domin tabbatar da ganin zaben ya gudana cikin yanayi mai kyau amma fa sai kun bamu hadin kai matuka idan dukkan mu muna son a asmu haka.
Shugaban na INEC ya kuma yi kira ga mutanen jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a kamar yadda jami’an tsaro suka baiwa hukumar duk wani tabbaci na samar da isasshen tsaro domin gudanar da zaben cikin lumana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bethrand Onuoha, ya kuma baiwa mazauna jihar tabbacin samun isasshen tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.
“A zabe, ba a amfani da adduna ko bindigogi don tilasta wa mutane su zabi abinda kake so. Irin waɗannan mutane idan muka kam su, za su gamu da fushin doka.
“Abin da muke so a Kogi shi ne a yi zabe cikin lumana. Don haka dole ne ‘yan siyasa su yi aiki bisa ka’idar zabe ko kuma mu yi maganinsu.
Discussion about this post