Shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC sun sanar da shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar nan ranar Talata 14 ga watan Nuwamba 2023.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwar kungiyoyin na musamman da aka yi ranar Talata a Abuja.
Manyan kungiyoyin kwadagon biyu sun ce an fara aika wa mambobi da kungiyoyi sakon soma shirin tsindima yajin aiki.
Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a makon jiya a jihar Imo.
Kungiyar Kwadago a ranar Juma’ar da ta gabata ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki biyar domin ta maye gurbin kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, yayin da ta kuma zargi Gwamna Hope Uzodimma da ke neman a sake zabensa a zango ta biyu da hannu a harin da aka kai wa Ajaero duk da cewa Gwamnan ya ce ba shi da hannu a harin kan shugaban kwadagon.
Kungiyar Kwadago, ta ce bayan haka lallai sufeto janar din ‘yan sanda ya hukunta wadanda suka ci wa Ajaero mutunci tunda wuri.
Discussion about this post