Kotun majistare dake Kaduna ta bada belin Felicia John akan naira 100,000 bayan an sameta da laifin saci naira 200,000 na saurayinta.
Alkalin kotun Ibrahim Emmanuel ya ce Felicia za ta kawo shaida daya dake zama a wurin da kotun ke da iko kuma shaidan zai gabatar da hotunan fasfo dinsa biyu a kotun.
Emmanuel ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 6 ga Disemba.
Dan sandan da ya shigar da karar Chidi Leo ya ce wani Michael Elisha dake zama a Sabon Tasha ne ya sanar da ‘yan sanda a ranar 3 ga Nuwamba da karfe biyar na yamma.
“Elisha ya ce budurwarsa Felicia dake zama a Agwan Maigero ta sace masa naira 200,000.
“Ya ce Felicia ta dauke masa kudin baya ta zo ta kwana a gidansa, bayan gari ya waye ya shiga bandaki sai Felicia ta dauki wayarsa ta tura kudin daga asusunsa na banki zuwa nata.
“Ya ce tun da ta yi haka ta gudu ba a sake ganinta ba sai da jami’an tsaro suka kamo ta.
Leo ya ce a hannun jami’an tsaro Felicia ta amsa laifint, sai dai ta ce wata bukata ce ta taso mata, sai dai kuma da ta tambaye saurayinta sai ya ki bata. Da ta samu dama sai ta tura kudin ta kama gaban ta.
Amma kuma da aka zo kotu sai Felicia ta musanta cewa ta aikata hakan kuma.
Discussion about this post