‘Yan bindiga sun kashe dagacen kauyen Zazzaga dake karamar hukumar Munya dake jihar Neja Usman Sarki sannan suka yi garkuwa da mutane da dama a kauyen.
Wani basarake a kauyen da baya so a fadi sunnansa saboda tsaro ya ce maharan sun kawo wa kauyen hari a daren Talata.
Ya ce maharan sun yi awon gaba da manoma da mata da dama a wannan gari.
“Zuwa yanzu bamu da masaniyar adadin mutanen da suka tafi da su daga kauyen kuma maharan sun kwashi dabbobi baya ga mutanen da suka sace.
Kakakin rundunar Ƴan sandan jihar Wasiu Abiodun shima ya tabbatar da haka sai dai ya ce bashi da cikakken bayanin abin da ya faru.
Jihar Nasarawa
Idan ba a manta ba a daren Litinin zuwa safiyar Talata ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu daliban Jami’ar Keffi dake jihar Nasarawa.
Katsina
Shugaban jami’ar Dutsen Ma a jihar Katsina Armaya’u Bichi ya ce ‘yan bindiga sun Yi garkuwa da daliban jami’ar mutum hudu.
Zamfara
Sannan a watan Satumba mahara sun yi awon gaba da dalibai 24 dake karatu a Jami’ar Gusau jihar Zamfara.
Mutane na da masu ruwa da tsaki na kira ga gwamnati da ta kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi a kasar nan.
Discussion about this post