Kasiloli 19 daga gundumomi a kananan hukumomi 23 dake jihar Kaduna sun canja sheka daga jami’yyar PDP zuwa jami’yyar APC.
Shugaban shirye-shirye na jami’yyar APC Kawu Yakasai da yake yi wa Kansilolin maraba ranar Talata ya ce wannan rana ce ta murna a jam’iyyar.
Ya tabbatar cewa APC za ta cigaba da tafiya da kowa da kowa sannan gwamnan jihar Uba Sani a matsayinsa na mutumin kirki zai kawo cigaba a jihar Kaduna da yardar Allah kowa ya ji dadi.
Da yake jawabi a madadin Kansilolin, Hon.Ishaku Ishaya Duchi daga gundumar Yelwa, karamar hukumar Chikun, ya ce sun yi farin ciki da manufofin gwamnatin Uba Sani na kyautata rayuwar mutanen jihar Kaduna.
Ya ce matakin da Gwamnan ya dauka na rage kudaden makaranta a Jami’ar Jiha da sauran manyan makarantun jihar, samar da aikin yi ga matasa, da raba kayan abinci kyauta da sauran ababen more rayuwa da ya hada da biyan matasa da talakawa alawus-alawus duk karshen wata sun yi tasiri ga rayuwar mutanen Kaduna.
“Wadannan da wasu dalilai ne suka sa muka yanke shawarar hada karfi da karfe da Sani domin kawo ci gaba a gundumomin mu da jihar baki daya.
Duchi ya ce kansilolin sun shawarci dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2023 Isa Ashiru ya yi watsi da zuwa kotu ya mara wa gwamnan jihar baya domin ci gaban jihar.
Idan ba a manta ba wasu gaggan ƴan PDP da ya haɗa da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero sun fice daga PDP bayan zaɓen 2023.
Ciki akwai Yakubu Lere, Tahir Tanko da wsu da dama wanda da su aka rika gwagwarmayar
PDP a baya.
Discussion about this post