Gunji Da Ƙarajin Raɗaɗin Tsadar Rayuwa A Abuja: “Ni fa da ka ke gani na a haka ɗin nan, ina da mota, amma tsadar fetur ya sa na ajiye ta a gida. Na gwammace na gwamutsu cikin irin wannan motar haya na zo aiki Abuja daga Gwagwala. Kuma na koma gida a takure a cikin irin wannan motar haya. Domin idan ba haka na yi ba, to zuwa aikin ba yiwuwa zai yi ba,” inji wani ma’aikacin Gwamnatin Tarayya mai suna Saliu Muhammad, wanda ke aiki a Ma’aikatar Harkokin Ilmi, a Abuja.
Salihu na zuwa aiki ne daga Gwagwalada, tafiyar kusan kilomita 58 daga Abuja.
Shiga irin ƙaramar motar hayar da Salihu ya shiga abu ne mai takura da matsatsi sosai, domin ana danƙara fasinjoji ne a bayan motar. Ga cinkoso, ga gumi, kuma ga tashin hamamin da ke fitowa daga jikin fasinjoji, musamman idan ana kartsa rana.
Irin yadda Salihu Mohammed ke gaganiyar rayuwa a Abuja a matsayin sa na ma’aikacin gwamnatin tarayya, haka miliyoyin mutane ke ci gaba da ɗanɗana kwankwasar da raɗaɗin tsadar rayuwa ke masu, tun bayan cire tallafin fetur.
Miliyoyin jama’ar da ke cikin wannan mawuyacin fili kuma na zaman tsammanin jiran-gawon-shanun tallafin gwamnatin tarayya. Mutane da yawa sun ajiye motocin hawan su saboda tsadar fetur.
Ƙalubalen Da Ke Gaban Majalisar Tarayya:
Ranar Talata ce mambobin Majalisar Tarayya za su koma majalisa domin ci gaba da aiki a matsayin su na Majalisa ta 10. Sun shafe makonni 10 su na hutu. Waɗanda suka yi hutu ko suka ziyarci yankunan su, sun ga irin yadda mutane ke gaganiyar rayuwa.
Kafin Majalisar Tarayya ta tafi hutu, ta gabatar da ƙudirin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa, amma kuma har yanzu lamarin bai yi wani tasiri ba, sai ma ƙara tsanani da ya yi. Har ta kai darajar Naira 1 ta yi lalacewar Dala ɗaya a Naira 1,000.
Har yanzu Majalisar Tarayya ba ta fito da ajanda ba. An dai kafa kwamitin bijiro da ajanda. Duk da da Shugaban Majalisar Tarayya Tajuddeen Abbas ya ce zai ci gaba ne daga inda tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya tsaya.
Akwai ƙalubale na tsaro a faɗin ƙasar nan, ga ƙalubalen raɗaɗin tsadar rayuwa da da sauran ƙalubalen da tilas sai Majalisar Tarayya ta tashi tsaye wajen bijiro da sabbin ƙudirori ga Shugaba Bola Tinubu.
Discussion about this post