Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ƙwato wayoyi har 890 daga hannun wasu ɓarayi, kuma ƴan wace matasa biyu.
A wani bidiyo da mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na Kano Abdullahi Kiyawa ya saka a shafinsa na Facebook an ga yadda aka yi baje wayoyin da kuma mutanen biyu da ake zargi.
Kiyawa ya ce an samu nasarar kama ɓarayin ne sakamakon kokari da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
Kiyawa ya ce dabarar da ake yi yanzu shine akan haɗa baki ne da wani ɗan shagon da ake sai da waya, wanda aka amince da shi , sai abuɗe shagon a wawushe wayoyin “a kwanakin baya ma an kama wani matashi da ake zargi da sato wayoyi 106 da komfutoci shida a wasu shaguna.
Ɗaya daga cikin matasan biyu da ake zargi da ƙanin mai shagon wayoyin ne, yayin da ɗayan kuma da suka ce shi ya sato makullin shagon, ƙanin manajan shagon ne.
Hakan ya sa hukumomi suka ja hankalin masu sana’o’i da su maida hankali matuka wajen sani waɗanda za su rika ba amanar dukiyoyin su.
Rundunar ƴan sandan ta ce kuɗin wayoyi 890 da ake zargin matasan sun sata ya kai naira miliyan bakwai.
A cikin bidiyon, an ga wadanda ake zargin da mai shekara 19 da mai shekara 23 suna bayanin yadda suka “sato” kayayyakin.
Shi ƙanin mai shagon ya ce wannan ne karo na uku da yake irin wannan aiki, inda a baya ya taɓa sayar da wayoyin da ya ce ya kwasa akan naira 500,000.
Discussion about this post