Sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya bayyana wa Majalisar Dattawa sabbin tsare-tsaren da zai fito da su, domin ƙarfafa darajar naira da hana darajar ta zubewa.
Ya ce ta haka ne zai sa masu zuba jari daga ƙasashen waje su samu ƙarfin halin daurewa su shigo da jari sosai, wanda hakan zai ƙara wa Naira ƙarfi har ta ji daɗin yin gogayya da dala ko sauran manyan kuɗaɗen waje da su ka fi ya daraja.
Mataki na biyu da Cardoso ya ce zai ɗauka, shi ne tirsasa bin ƙa’idojin da doka ta tanadar wajen samar da canjin kuɗaɗen waje ga masu zuba jari.
Cardoso wanda tsohon Shugaban Citibank ne, yi bayanai a lokacin da Majalisar Dattawa ke tantance shi, tare da amincewa da shi a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).
An naɗa Cardoso a daidai lokacin da Najeriya ke cikin wani mawuyacin hali, inda Dalar Amurka ɗaya ta kai Naira 1,000 cur.
Wannan taɓarɓarewar darajar Naira ya ƙara sa masu son zuba jari daga ƙasashen wajen na tsoron shigowa yin waya hada-hada ko kafa masana’antu a Najeriya.
A ɗaya bangare kuma tattalin arzikin cikin gida na ƙara fuskantar barazana sanadiyyar tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa da tsadar kayan abinci waɗanda suka haddasa raɗaɗin tsadar rayuwa, tun bayan cire tallafin fetur a ranar 29 ga Mayu.
Harkoki sun samu tawaya saboda tsadar harkokin sufuri, biyo bayan ƙarin kuɗin fetur da aka yi.
A Najeriya, an bayyana ra’ayin cewa idan ba a biya bashin dala biliyan 6.8 ɗin da ya hana CBN faffaka ba, to samun nagartaccen tubalin gina tattalin arziki ba zai yiwu ba.
Najeriya ta karya darajar Naira da kashi 40% bisa 100 bayan hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Ɗaukar Csrdoso matsayin Gwamnan CBN ya jefa fargaba a zukatan wasu masana, waɗanda ke cewa ya fito ne daga bankin kasuwanci, riba kaɗai ya sani amma bai san dabarun tsara tattalin arzikin ƙasa ba.
Discussion about this post