Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya nada kwamitin mutum Takwas su bi diddigin kwangilolin da tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ba da a lokacin mulkin sa a Kaduna.
A wata sanarwa wanda Sakataren Yada Labarai na gwamnan jihar ya fitar ranar Litinin, gwamna Uba Sani ya ce kwamitin za ta bi diddigin duka ayyukan da ake yi yanzu ba a gama sannan kuma za a yi wa takardun bada kwangilolin ayyukan filla-filla domin sanin inda aka kwana.
Cikin ayyukan da kwamintin za su yi sun hada da, Kayyade matsayin dukkan ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar, samun cikakkun bayanai game da yarjejeniyar bada kwangilolin, Sanna kuma su bankado yadda aka tsara za arika biyan ‘yan kwangilan da kuma halin da ake ciki zuwa yanzu.
” Sannan kuma su binciki yaushe ne wa;adin kammala akowani aiki da kuma shawarwari ga gwamnati.
Mamabobin kwamitin da aka nada sun hada da:
a. Sabiu Sani, Special Adviser, Investment & Promotion – Chairman
b. Dr. Abdullahi B. Ahmed, Special Adviser, Project Monitoring, Implementation and Result Delivery – Member
c. Dr. Mustapha Musa, Special Adviser, Legal – Member
d. Fabian Okoye, Special Adviser, Research, Documentation & Strategy – Member
e. Ibrahim T. Muhammad, Special Adviser, Economic Matters – Member
f. Atiku Sankey, Special Adviser, Peace and Conflict Resolution – Member
g. Larai Ishaku – Member
h. Shuaibu Kabir Bello, Senior Special Assistant, ICT – Secretary
Discussion about this post