Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya zazzagaya cikin garin Kaduna domin jin yadda kasuwar raguna ke gudana, abinda ya gano kuwa sun ba shi mamaki da tsoro kaɗan.
Domin wasu ragunan sun yi tsadar da basu taɓuwa, wasu kuma za ka same su daidai misali dai za a iya yin layya dasu.
A wasu kasuwannin ragunan, akwai ƴan ƙananan rago wanda za aiya samun su a naira 50,000 da ƴan kai. Wasu kuma sun fi haka.
Da yawa waɗanda ake samu da arha duk da dai ƙanana ne akan yi musu suna da kiwon gida, wato kodai wani manomi ya daure abar sa yana ta kiwo har sallah yanzu ya siyar da su.
Haka kuma akwai Tunkiya, da akuya wadanda suma ana yin layya da su, kuma sun fi ragunan saukin kuɗi.
Wuraren da za aka sa yi rago da saukin kuɗi a Kaduna syn haɗa da:
1 – Babbar Kasuwar dabbobi na Zango, Tudun wada Kaduna.
Duka da tsadar dabbobi da ake fama da shi, a kasuwar zango, na Rudun Wada Kaduna, za ka samu kananan dabbobi waɗanda sun kai a yi layya da su cikin kuɗi daidai. Akan samu har na naira 50,000 da ƴan kai.
2 – Kasuwar Ƴan Tumaki dake Kawo Kaduna
A kasuwar Ƴan tumaki dake Kawo shima ya shahara wajen saida dabbobi. Wakilin mu ya gano cewa akwai dabbobi masu kananan kuɗi wanda mai niyyar Layya zai iya siya yayi layya.
3 – Sai kuma masu zazzagaya wa da raguna a hannu.
Suma idan ka ci karo da sa’a, za ka samu rago mai saukin kuɗi da za aka iya siya domin layya a hannun su.
4 – Kauyukan da ke kewaye da Kaduna
Akwai kauyuka da rugage da ke kewaye da Kaduna wanda mutane kan garzaya har can su siya raguna da arha. Idan zaka oya ka kokarta ka tafi ire-iren waɗannan ƙauyuka, za ka samu dabba da sauki.
Discussion about this post