A ranar Asabar ne aka afka cikin ruɗani da cikin jirgin saman Ibom Air inda wani fasinja jirgin ya furta cewa ba za a rantsar da Tinubu shugaban kasa a Najeriya ba.
Shi dai wannan fasinja ko da ya shiga cikin jirgin a daidai zai zauna sai ya waiwayi fasinjoji da ke zaune ya ce musu ” Kalle ku duka, haka za ku rika zama kuna kallo za a rantsar da Tinubu shugaban kasa, Ba za mu yarda a rantsar da shi ba.
Daga nan ne fa wasu daga cikin fasinjojin suka rika cewa ba a cikin jirgin sama za ka rika yi mana irin wannan barazanar, ka tafi kotu idan baka yarda da zaɓen ba.
Haka kuma suka roki jami’an tsaro dake kula da wannan jirgi da su fidda shi daga jirgin.
Ko da ya ke wannan fasinja ya turje cewa ba zai fita a lokacin da aka umarce shi ya fice cikin arziki, daga baya dai sai da aka yi masa taron dangi a ka fidda shi da karfin tsiya.
Zuwa yanzu dai an yana tsare a hannun mahukuntan Najeriya a na yi masa tambayoyi.
A lokacin da ake kokuwar fidda shi daga jirgin, ya rika kiran sunan magoya bayan dan takarar LP wato Obidients, su kawo masa ɗauki.
” Ina kuke ƴan Obidients, Ku kawo ɗauki, kun ga abinda ake yi mini.” Haka ya rika cewa.
Tun bayan nasarar da Tinubu yayi a zaɓen shugaban kasa, magoya bayan LP suke ta tada jijiyoyin wuya suna zargin an yi musu murɗiya a zaben ne. Peter Obi na LP ne ya lashe zaben.
Discussion about this post