Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya maida wa zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Abba Yusuf martani cewa ya taka a hankali, domin har yanzu Ganduje ne gwamna.
Ganduje ya ce Abba ya daina fitar da sanarwar bayar da umarni, saboda ba a kai ga rantsar da shi ba. A cewar Ganduje, har yanzu ikon mulkin Kano na hannun sa, ba hannun zaɓaɓɓen gwamnan ba.
Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Muhammad Garba ya fitar a ranar Juma’a.
Gwamna Ganduje ya fitar da sanarwar a matsayin raddi ga wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano ya fitar a madadin sa.
Sanusi Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a madadin Abba Gida-gida cewa duk wanda ya sa san ya na gini a wasu wurare mallakar gwamnati da aka lissafa a takardar, to su gaggauta dakatar da ginin.
A ranar Alhamis ce Abba ya gargaɗi ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiya su daina ci gaba da gine-gine a wasu keɓantattun wuraren da su ka saya a hannun gwamnatin Kano.
“Ana gargaɗin waɗanda su ka sayi filaye a hannun gwamnatin Kano a wuraren da su ka haɗa da makarantu, masallatai, wuraren inganta al’adun Hausawa, asibitoci, maƙabartu da kuma jikin ganuwar Kano, cewa su daina gini.”
Martanin Ganduje
Gwamna Ganduje ya shaida wa Abba cewa ya na da ikon da zai raba filaye kamar kowane gwamna ga jama’a.
“Gwamnonin jihohi na da iko mai ƙarfi na raba filaye, kuma kowace gwamnati ta raba wa jama’a filaye, ciki har da gwamnatin da ta gabata, wadda Abba ya yi Kwamishina a lokacin mulkin Gwamnantin, wato ta Rabi’u Kwankwaso.
“Kuma rekod ya nuna cewa gwamnatin da ta gabata ta raba filaye har a wuraren da zaɓaɓɓen gwamna ya ce wai a dakatar da gine-gine a yanzu. Ciki kuwa har da jikin ganuwar Kofar Nassarawa da Ƙofar Mata, sai kantina a Ƙofar Mata, Filin Idi masu kallo Orion Cinema, daga Kofar Mata zuwa ‘Yan Yashi, masu kallon filin Idi da kuma Ƙofar Kabuga zuwa Ƙofar Famfo masu kallon Jami’ar Bayero.
“Shawarar daina ginin da zaɓaɓɓen gwamnan ya bayar ta haifar da ruɗu a Kano, don haka ya daina wannan azarɓaɓin.”
Ganduje ya ce duk wanda ya san ya sayi filin bisa ƙa’ida, kada ya yi wata fargabar komai.
Abba dai ya yi Kwamishinan Ayyuka a zamanin mulkin Kwankwaso.
Ganduje ya ƙara nanata cewa har yanzu shi ne gwamna, shi kuma Abba sai a ranar 29 Ga Mayu za a rantsar da shi.
Discussion about this post