Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Atiku Abubakar da ke PDP, ta yi kira ga Hukumar NDLEA ta gaggauta binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu dangane da zargin harƙallar muggan ƙwayoyi da aka yi masa tun tuni.
Sanarwar da rundunar yaƙin ta fitar ta bayyana cewa ganganci ne babba kuma mummunan kuskure za a tafka, idan aka zaɓi wanda aka zarge shi da tu’ammali da muggan ƙwayoyi ƙiri-ƙiri a cikin 2013.
“Idan aka bari ya zama shugaban ƙasa, to Najeriya za ta afka cikin muggan laifukan da manyan ‘yan ƙwaya ke haddasawa.
“Najeriya za ta yi kuskure idan aka zaɓi mutumin da ake zargi da harƙallar muggan ƙwayoyi. Kada a kuskura a yi sakaci har ya zama shugaban ƙasa. Domin Najeriya za ta iya komawa hannun ‘yan ƙwaya, wadda zasu riƙa tafka muggan laifukan da za su lalata Najeriya fiye da yadda aka yi wa Colombiya.”
Ita ma APC ta ce Atiku ba shi da nagartar da zai iya riƙe amanar Najeriya.
Jam’iyyar APC a ƙarƙashin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ba abin bai wa amanar riƙon Najeriya ba ne.
Kakakin Kamfen ɗin TInubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Abuja, a ranar Lahadi.
Onanuga ya ce kamata ya yi NDLEA ta kama Atiku Abubakar ta bincike shi dangane da zargin harka da muggan ƙwayoyi da aka yi masa a cikin wani faifan murya da aka watsa a makon jiya.
Haka kuma ya yi kira ga EFCC ta gayyaci Atiku Abubakar dangane da zargin harƙallar maƙudan kuɗaɗe da duk dai wani mai suna Micheal Achimugu ya yi wa Atiku.
Achimugu ya shafe makonni biyu ya na watsa bayanan da ke ɗauke da zarge-zargen harƙallar da ya ce Atiku ya yi a lokacin da ya ke Mataimakin Shugaban Ƙasa, tsanakin 1999 zuwa 2007.
Achimugu ya yi iƙirarin cewa ya taɓa yin aiki a hannun Atiku, a matsayin hadimin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Idan ba a manta ba, ita ma jam’iyyyar PDP ta zargi Bola Tinubu, ɗan takarar APC da haifin harƙalla da muggan ƙwayoyi a cikin 2015.
Kusan manyan jam’iyyun guda biyu dai, wato PDP da APC sun saki layin kamfen kan alherin da za su shuka idan aka zaɓe su, sun karkata zuwa ga kamfen ɗin yarfe kan ‘yan takarar su na shugaban ƙasa, wato Atiku Abubakar na PDP da kuma Bola Ahmed Tinubu na APC.
Discussion about this post