Wasu mazaunan jihohin Zamfara da Sokoto sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 15 sannan wasu da dama sun ji rauni a bayan harin da ‘yan bindigan suka kai a wasu kauyukan jihohin.
Kauyukan da maharan suka kai wa hari sun hada da Ruwan Bore dake jihar Zamfara da Gatawa, Dangari and Kurawa dake jihar Sokoto.
Wani mazaunin kauyen Dangari dake jihar Sokoto Nura Mamman ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun dira kauyen ne da misalin karfe biyu na rana.
“Ina zaune a cikin gidana sai na ji ihun mata da yara kana ashe lokacin maharan ne ke kokarin shigowa amma jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da ‘yan banga na kokarin hana su shigowa kauyen.
“Ka san sukan raba kansu zuwa gida biyu ne ko fiye da haka amma a wannan karon maharan sun zo da yawa dauke da manyan makamai da hakan ya sa jami’an tsaron ba su iya hana du gigowa garin ba.
Mamman ya ce a lokacin da suka shigo kauyen mafi yawan mazauna kauyen sun gudu zuwa wasu kauyukan dake kusa da su.
Ya ce maharan sun kashe mutum hudu sannan wasu mutum 10 sun ji rauni.
Daga nan gidan jaridar ta samu bayanin cewa maharan sun Kai wa kauyukan Gatawa da Kurawa dake karamar hukumar Sabon Birni hari.
Mazaunin karamar hukumar Isa kuma Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ‘Rundunar Adalchi’ Basharu Guyawa ya ce bisa ga lissafin da aka yi ‘yan bindigan sun kashe mutum 11 sannan da dama sun ji rauni daga wadannan kauyuka.
“Yanzu mutane sun fara sabawa da hare-haren ‘yan bindiga domin maharan da rana tsaka suke kawo wa mutane hari ba tare da fargaba ko tsoron jami’an tsaro ba.
“Zuwa yanzu maharan sun kashe mutum 11 sannan akalla akwai mutum takwas da suka ji munanan raunuka suna kwance a asibiti.
Guyawa ya tabbatar cewa lalle jami’an tsaro sun Yi batakashi da maharan amma maharan sun fi karfinsu saboda yawan su da karfin makaman da suke dauke da su.
Jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun kashe mutum hudu sannan mutum 10 sun ji rauni a jikinsu a kauyen Ruwan Bore dake garin Gusau.
Wani mazaunin kauyen da baya so a faɗi sunnan sa ya ce maharan sun shigo kauyen su da yammacin Litinin ne.
“Da kyar na tsira da raina sannan mata da yara kananan sun gudu zuwa kauyen Kwatarkwashi domin samun mafaka. Mu mazan ne kawsi muke kauyen domin yi wa wadanda aka kashe jana’iza .
Ya Yi kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen damar wa mutane tsaro a jihar.
“A kwanakin baya ‘yan bindiga sun sakawa kauyen Gora harajin Naira miliyan hudu sannan suka zo kauyen da babban mota inda suka sace hatsi har buhu 130 suka loda a motar sukayi gaba.
Discussion about this post