Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ƴan takarar shugaban kasa na APC wato Bola Tinubu da na PDP Atiku Abubakar duk ruɓaɓɓun ƴan siyasa ne duk sun gaji.
A hira da ɗan takarar yayi da radiyon Alfijir, ya yi musu kakkausar suka ga takarar Atiku Abubakar na PDP da Bola Tinubu na APC.
Kwankwaso ya ce: Mutanen nan sun gaji mutanen nan ba za su iya ba, kawai ƙaraƙara suke yi. Wasu daga cikin su za ka ga ramarama suke yi, wandunan su a jike kamar yara, wato tafiya ta yi tafiya a rayuwa.
Kwankwaso ya ci gaba da yi wa ƴan Arewa gargaɗin kada su yi kuskuren sake zaɓen wanda zai gasa musu wuta a hannu.
” Nan ake ta surutai game da su takardun karatunsu, wannan yayi kaza wancan bai yi kasza ba. Ni dinnan PHD na ke da shi. Tun kafin in zama gwamna nake aiki wa mutanen Kano, ina ta hada wa Kanawa ruwa, daganna na zama gwamna, ba su kai ni ilimi ba da cancanta.
Kwankwaso ya ja hankali da kira ga ƴan Najeriya su tabbata sun zaɓi nagari wanda ,ai ji tausayin su ya kuma samar musu da ababen more rayuwa sannan kum mai kishin su.
Discussion about this post