Hamshakin attajiri, kuma dattijon Arewa, Aminu Ɗantata ya bayyana cewa yanzu duniyar ma yana binta ne sannu a hankali amma ba daɗinta ya ke ji ba.
Ɗantata wanda shine kawun Aliko Dangote ya ce lokaci kawai ya ke jira amma ba bu kuma sauran abin da ya rage masa kuma.
” Ni din nan ina da abokan a faɗin kasarnan a duka jihohin Najeriya, amma ina tabbatar muku babu mutum 10 da suka rage suna raye yanzu.
Ɗantata dake da shekaru 91 yanzu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, bayan ɗan takarar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kai masa ziyara a Unguwar Koki dake Kano.
” Tsakanina da Allah bana jin daɗin duniyar nan yanzu, komawa ta ga Allah shine kawai na ke jira yanzu. Fata na shine Allah ya sa mu gama da duniya lafiya.
” Bayan haka kuma ina rokon duk wanda na yi wa laifi ya yafe mun, nima duk waɗanda suka yi min na yafe musu.
” Yanzu ni kaɗai ne na rage cikin ƴan uwana kaf, sai tarin jikoki da nake tare da su.
Ɗantata mashahurin attajiri ne mazaunin garin Kano wanda ya gaji arziki. Mahaifinsa, Alhassan Ɗantata, ya taba zama wanda ya kowa tarin dukiya a yankin Afrika saboda fice da yayi a harkar kasuwanci.
Discussion about this post