‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe biyu na APC sun fice daga jam’iyya mai mulkin jiha, sun koma NNPP.
Honorabul Hamza Adamu mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Balanga ta Kudu, ya watsar da ɗaurin tsintsiya shi da Honorabul Bappah Usman mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Funakaye ta Kudu, sun rungumi kwandon kayan marmari.
‘Yan Majalisar su biyu waɗanda a yanzu haka su na kan muƙaman su, sun yanke shawarar komawa NNPP ne bayan wata keɓantacciyar ganawar da su ka yi da ɗan takarar gwamnan Gombe na NNPP, Khamisu Mailantarki.
Su biyun sun canja sheƙa zuwa NNPP, sa’o’i kaɗan kafin fara ƙaddamar da kamfen ɗin Mailantarki na takarar gwamna a ranar Asabar.
Da su ke ganawa da manema labarai,
Bappah Usman da Hamza Adamu sun bayyana cewa sun koma NNPP domin sun haska sun hasko cewa ‘yan takarar gwamnan Gombe na APC da PDP duk ba su da wata natija ko gogewar da za su iya kawo wani ci gaban da Gombawa za su yi alfahari da su.
Sun ce su na da yaƙinin cewa Mailantarki ya fi sauran cancanta da kishin al’ummar sa.
NNPP na ci gaba da ƙara samun tagomashi a Jihar Gombe, ta yadda ake ci gaba da shiga jam’iyyar daga jam’iyya mai mulki da jam’iyyar adawa PDP.
Kwanan nan ma Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Kamfen ɗin PDP a Gombe, ya jefar da laima, ya rungumi kwandon kayan marmari.