Duk ranar 9 ga watan December, Majalissar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da cin hanci da rashawa ta duniya.
Mutane sun gaza fahimatar cewa. Cin Hanci da Rashawa kusan shine ummul aba isin din matsalolin da kasar ke fama da ita. Wannan matsala ita ta kara tasirin masifar rashin tsaro, ta tura miliyoyin ‘Yan Nijeriya cikin kangin talauchi, rashin shugaban ci na gari, wannan masifa ta yi naso daga kasa har sama.
Abin takaicin shine yadda ‘Yan Nijeriya suka yi imani da yarda da cewa Cin Hanci da Rashawa da tara dukiya ta yaki-haram, yaki-halal it ace kadai mafuta a wannan rayuwa ta Nijeriya, wannan ya saka, zai yi wahala a samu wani bangare na wannan kasa da babu dattin cin hanci da rashawa.
Hatta a makarantu a kan bada cin hanci don a ci jarabawa, a kan bada hanci domin samun guraben karatu a manyan makarantu, a kan sayi takardar kama aiki a ma’aikatun gwamnati, kuma abin ban haushin mutane sun yarda dole sai anyi haka sannan za a rayu.
Yau fa, a wurin mutane babu wani mai daraja sai mai tarun kudi, walau kudin halal ne ko haram ne, babu mai kima ko mai daraja sai mai kudi, saboda haka, kowa yake kallon sata da tara kudi, itace kawai mafuta.
Babban abin takaici shine yadda a kwanakin baya Shugaba Buahari yake nuna cewa, Yan Nijeriya sun dibga cikin talauci ne, saboda gwamanonin kasar suna karkatar da kudin kananan hukumomi, yadda ya biya misalin cewa in a kabawa karamar hukuma N100M sai su kwashe rabi su basu rabi, da ma an jima ana wannan rade-radi sama da fadi da kudin kananan hukumomi.
Abin tambaya ma anan shine, wai akwai demokaradiyya a cikin zaben kananan hukumomi a Nijeriya, shin ma a kwai yanci da bibiya wajen yadda a ke gudanar da kananan hukumomi a Nijeriya?
Wannan ba shine kadai abin mamakin ba, kamar yadda gwamnatin tarayyar ke kalubalantar gwmanonin jahohi kan kasa habbasa na kawar da talauci, sun maida hankali wajen yin aiyukan da ba zai taimaki mutanen karkara ba, a yayin da suma suke maida martanin cewa shugaban kasar ya kasa cika alkawuran sa a kan ‘Yan Nijeriya, wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da tsaro.
Ko ma wanene zai jagoranci kasar nan zai sha wahala wajen yakar rashawa domin yan kasar sun yi imani da cewa rashawa da tara kudi ta kowane hali ita kawai mafita ba tare da la’akari da masifar da ke ciki ba.
In mukayi duba da yadda a ka kashe makudan kudi a kwanakin baya wajen fidda ya takarkarun manyan jama’iyun kasar nan na APC da PDP, ta yadda a ke rade-radin bawa Delegate kimanin N3M ko ma sama da haka don sayan kuri’ar sa wajen zabar dan takarar shugaban kasa.
Wannan karara ya nuna yadda shugabanni da magoya baya suka yi imani da cin hanci da rashawa. Wannan ya tuna min wata hira da mukayi da wasu delegates din na wata jaha a arewacin Nijeria, yadda suke zargin jagororin su da yi musu zare a cikin kudin da a ka basu, wato sata cikin sata. To koma menene wannan ne dabi’un yan siyasa kenan da suke son mulkar kasa kamar Nijeriya.
Imanin Yan Nijeriya a kan cin hanci da rashawa, yau babu wani mai tsayawa takara sai ya sayi kuri’a a gun masu zabe, abin takaicin ma irin wannan lamari ba a boye a ke yin sa ba. Yau dan siyasa sai ya tara kudi ta kowane hali in har yana so a zabe shi, domin nagartar sa a wurin mutane shine, nawa zai basu.
Saboda imanin ‘Yan Nijeriya a cin rashawa, yau fa ana saida man fetur sama da naira 300, sabanin kudin sa na hakika na naira 165, duk da cewa a wannan shekarar kadai gwamnati ta kashe sama da naira Trilion 6 a kan bada tallafin man fetur. Amma mutane sun gaza fahimtar cewa, shi cin hanci da rasahwa yana kashe karkasin doka, ko yanzu mutane sun fahimta, kusan gwamnati ta kasa komai a kan wannan lamari.
Abin damuwa ma, shine yadda a kwanakin baya a ka rawaito takaddama tsakanin Ministan Kudi da Shugaban NNPCL da kuma Shugaban Custom na Kasa wato Hamid Ali a kan ainishin yadda a ke kashe wannan magudan kudi a kan tallafin man Fetur. Amma babu wani abin da ya shalli yan Nijeriya a kan wannan badakala.
Kai rashawa ta hana Nijeriya cin moriyar arzikin man fetur, yau rashin tsaro da rashawa ya sanya Nijeriya bata iya hakko adadin fetur din da OPEC ta yarde mata. Wai dan Allah zaka iya hada Nijeriya da kasshe irin su Qatar da Saudiya wajen cin moriyar arzikin man fetur?
Saboda da haka duk al’umar da suka yadda, tara kudi ta kowane hali da karbar rashawa wani abuni mai muhimmanci a rayuwar su, zasu kasance cikin kaskanci da kuma mummunan jagoranci. Rashin tsaro da rashin ingancin rayuwa zai yi ta karuwa.
Allah ya kauta.
alhajilallah@gmail.com