Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata a Abuja, ya gargadi ministoci, sakatarorin dindindin da shugabannin hukumomin gwamnati da kada su yi watsi da ayyukan su su bi ayarin Kamfen.
Shugaba Buhari ya bayar da umarnin ne a wajen rufe taron bitar ayyukan ministoci na shekarar 2022, kafin ya rattaba hannu kan Dokar Zartaswa mai lamba 012 kan Inganta Ayyukan Gudanar da ayyuka.
Shugaban ya shaida wa mahalarta taron cewa tun da aka fara yakin neman zaben 2023, dole ne harkokin gudanar da mulki su ci gaba da samun kulawar da ake bukata a wannan lokaci.
“Saboda haka, ina horon dukkan ministoci, sakatarorin dindindin da shugabannin hukumomi dole su mai da hankali wajen gudanar da ayyukansu, domin idan aka samu akasin haka za a hukunta mutum.
Shugaba Buhari ya kuma umurci sakataren gwamnatin tarayya da ya ci gaba da gudanar da bita da tantance ma’aikatun gwamnati a zango na uku da hudu na shekarar 2022, yana mai cewa rahotannin za su kasance wani bangare na takardun mika mulki ga gwamnati mai zuwa.
A karshe shugaban Buhari ya yaba wa kwazon sakataren gwamnatin tarayya da tawagarsa bisa nasarar shirya wanna taro na bita da aka yi yana mai cewa da fatan wadanda akayi domin su za su dau darasi.
Discussion about this post