Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya zargi dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi cewa ya taba saka jam’ian tsaro su tsare shi da karfin tsiya a dakin Otel din sa alokacin zaben 2014, wato lokacin tah Obi ke gwamnan jihar Anambra.
Wannan korafi ya tada hayayaga a shafukan jaridu da sada zumunta.
El-Rufai yace ” Obi na gwamna ya sa aka tsare ni a dakin Otel din da nake ciki a Anambra da karfin tsiya. Yanzu ni ne gwamna a Akaduna kuma shima ya zo Kaduna, ashe zan iya ramawa, tunda ni ba ma yan sanda ba har runduninin sojoji ina da su a Kaduna. Sai dai kash, ni dan Arewa ne ba mu gaji haka ba. ina maka fatan Alkahiri a ziyarar ka Kaduna.
A martanin da ya maida wa El-Rufai, Peter Obi ya ce ” Mutane irin su El-Rufai addu’a kawai ake yi musu, domin sun rika sun nausa can kololuwa basu jin kira. Ni ban saka a tsare shi a Anambra lokacin da nake gwamna ba.
” Hasali ma a lokacin ni Ina APGA ne, PDP ce ke mulki a Abuja, sannan duk jami’an tsaron dake kewaye da ni ‘yan Arewa ne. Ba saka a tsare shi ba. Shi dai da ya saba surutu ba birki sannan baya tauna kafin ya amayo abinda yake so ya fadi mishi can.
“Abin da nake yi wa mutane irin su El-Rufai shi ne in yi musu addu’a tare da kwadaitar da su su maida hankali wajen yin abubuwan da za su kyautata wa ‘yan Najeriya fiye da yin kalaman kiyayya da za su raba kan kasar da kuma lalata kasar,”
Discussion about this post