Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya ƙaddamar da sabunta takardun naira, a ranar 15 Ga Disamba, 2022.
CBN ya ce zai canja launin takardun kuɗin ne domin ya yi wa kuɗaɗen da ke hannun jama’a talala, sannan kuma ya taka wa tsadar rayuwa burki.
Wani dalilin kuma da CBN ya bayar, shi ne za a canja wa kuɗaɗen launi ne domin a magance babbar matsalar yawaitar kuɗaɗen jabu.
CBN dai ya yi shirin sauya launin takardar Naira 100, Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 1000.
Sabbin kuɗaɗen za su fara shiga hannun jama’a a cikin Disamba. Daga nan kuma a cikin Janairu, 31 Ga wata, 2023 za a daina amfani da tsoffin da a yanzu ke hannun jama’a.
Yayin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ke wa manema labarai bayani a ranar Laraba, ya ce CBN ya sha fama da ƙalubale daban-daban, wanda ya zama barazana ga martabar CBN da martabar Najeriya baki ɗaya.
“Matsalolin da ƙalubalen sun haɗa da kimshe maƙudan kuɗaɗe da jama’a ke yi ba tare da ana juya su ba.”
Ya ce an gano cewa kashi 85% na kuɗaɗen da ake jalautawa a hannun jama’a ba su shiga asusun CBN.
“Ya zuwa cikin watan Satumba,2022, alƙaluman ƙididdiga sun tabbatar da cewa naira tiriliyan 2.73 daga cikin naira tiriliyan 3.23 ɗin da ke juyawa a hannun jama’a, ba su cikin rukunin talalar bankunan ‘yan kasuwa, wato duk su na hannun jama’a.
“Sannan kuma hujjoji sun tabbatar da cewa hakan ya na ƙara haifar da tsadar rayuwa da tsadar kaya, lamarin da rabon da a samu hauhawar farashi sosai kamar bana, tun shekaru 17 da su ka wuce.
Ya kara da cewa ana samun yawaitar ruɓaɓɓu da rududdugaggun kuɗaɗe a hannun jama’a. Kan haka ne ya ce ƙarancin takardun kuɗaɗe masu kyau, marasa datti na rage wa CBN kwarjini. Sannan kuma ya na haifar da tangal-tangal ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce sauya launin takardun nairori zai rage yadda ake kinkimar maƙudan kuɗaɗe buhu-buhu ana kai wa masu garkuwa domin biyan diyya.
Sai dai kuma tuni jama’a sun shiga damuwa da ruɗani, musamman idan su ka tuna irin bala’in da aka fuskanta, cikin 1984 lokacin mulkin Buhari na soja, lokacin da aka yi canjin kuɗi.
Discussion about this post