Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na PDP Isah Ashiru ya bayyana cewa ba shi tantamar cewa tun kafin 12 rana ranar zaɓe PDP za ta yi dagadaga da APC a jihar gabaɗaya a ɓarke da bikin nasarar PDP a jihar.
Ashiru ya faɗi haka a lokacin da ya ke jawabi ga dubban magoya bayan jam’iyyar ciki har da daruruwa da suka canja sheka daga APC zuwa PDP a karamar hukumar Giwa.
Ashiru ya ce ” Ina muka albishir cewa jam’iyyar mu ta PDP, jam’iyyar ce da zata dawo da martabar jihar Kaduna kamar yadda ta ke a ada.
” Idan Allah ya yarda, muna fatan kafin karfe 12 rana mutanen jihar Kaduna za su ɓarke da biki da murnar nasarar da za mu samu, ‘wato na yin kuli-kukin kubara da APC a zaɓe a jihar.
Honarabul Ashiru ya sah yin soka kan irin yadda a cewar sa gwamnatin APC ta mulki mutanen jihar Kaduna.
A hira da ya yi da talabijin ɗin Arise ya ce ” Babban burina idan na zama gwamnan Kaduna shine in haɗa kan mutanen jihar wato in kawo karshen banbance banbancen da ya raba haɗin kan mutanen jihar.
Ya kara da cewa, zai bi ayyukan da gwamnatin da ta shuɗe ɗaya bayan ɗaya waɗanda suke da kyau a kyale su waɗanda kuma sai yi musu gyara da garambawul ayi musu.
A karshe Ashiru ya ce mutanen Kaduna ba za su yi da na sanin zaɓen jam’iyyar PDP a jihar ba idan har Allah ya ba shi sa’a ya zama gwamnan jihar.
Discussion about this post