‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a New Haven dake karamar hukumar Enugu ta Arewa jihar Enugu.
Maharan sun kai wa jami’an tsaron hari da misalin karfe 10:25 na daren Laraba.
‘Yan bindigan sun bude wa ‘yan sandan wuta da hakan ya yi ajalin mutum uku sanadiyyar wannan hari.
Wani mai shagon daukan hoto dake kusa da wurin da baya so a fadi sunan sa ya ce maharan sun yi tattakin musamman domin kai wa
“Mun tsinci gawar ‘yan sanda biyu amma mun samu labarin cewa an kai daya asibiti.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Daniel Ndukwe wanda ya tabbtar da harin ranar Alhamis ya ce maharan dake cikin mota mai Kiran Lexus SUV sun ka wa jami’an tsaron dake yawon stir hari inda ‘yan sanda uku suka ji mummunan rauni.
Ndukwe ya ce an yi gaggawar kai jami’an tsaron asibiti inda likita ya tabbatar cewa sun mutu.
Ya ce tuni dakaraun ‘yan sanda sun fantsama domin kamo wadannan ‘yan bindiga domin a hukunta su.
Jihar Enugu na daga cikin jihohin yankin Kudu maso kudancin kasar nan dake fama da aiyukkan ‘yan bindiga.
Maharan na yawan kai wa jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati hari wanda ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne suka kai wannan hari.
Discussion about this post