Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi dadewa a sarautar Birtaniya, ta rasu tana da shekaru 96.
Sarauniya Elizabeth ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.
BBC HAUSA Ta buga cewa iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis.
Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama.
Babban danta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.
A sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: “Sarauniya ta rasu salin-alin a Balmoral da rana.
An haifi Elizabeth Alexandra Mary Windsor a ranar 21 ga Afirilun 1926, a wani gida da ke gefen dandalin Berkely a Landan,inda ta kasance ‘ya ta farko ga Albert, Basarake Duke na York, wanda shi ne da na biyu a wajen Sarki George V da maidakinsa, mai lakabin martabar sarauta ta Duchess, wadda a da sunanta ُ Elizabeth Bowes Lyon.
Elizabeth da ‘yar uwarta Margaret Rose, wadda aka haifa a shekarar 1930 sun yi karatu a gida, karkashin kulawar zuri’arsu a yanayi mai annashuwa da nuna kauna. Elizabeth ta samu matukar kusanci da mahaifinta da kakanta George V.
Tana da shekara 6, Elizabeth ta fada wa mai ba ta horon sukuwar doki, cewa, ‘tana da burin zama mace mai kimar matsayin daraja da ta mallaki dawakai da karnuka.”
An bayyana cewa ta nuna alamun iya jan ragamar al’umma tun tana karama. Winston Churchill, wanda a zamanin yake hankoron zama Firayiministan kasar, an jiyo daga gare shi, cewa, “tana da kwarjinin mulki, al’amarin da ke da ban mamaki ga yarinya karama.”
An samar da kungiyar ‘yan mata masu aikin agaji na “Girl Guides” irinta ta farko a fadar Buckinhgham, wadda aka kafa da manufar (Elizabeth) ta saba mu’amala da rukunin ‘yan matan da ke matakin shekarunta.
Discussion about this post