Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC Bola Tinubu ya bayyana cewa ƙarya tantagarya da aka buga wani labari cewa an samu saɓani kuma ba ya jituwa shi da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu.
Tinubu ya bayyana haka a ranar Laraba, lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Sakateriyar APC, a Abuja.
Yayin da manema labarai su ka yi masa wannan tambayar, sai Tinubu ya ce, “ƙarya ce tsagwaron ta. Masu ƙirƙirar ƙarya ne kawai ke shafta ta, amma dai babu wani saɓani tsakani na da Adamu. Kowa ya san mun daɗe tare da juna ni da shi. Saboda haka nan damu da dukkan masu faɗar abin da ran su ke so ba su yi ta faɗa.
“Shi dama mai rawa har jama’a su gani, ai a kasuwa ya ke yin rawar sa, ba cikin keji ba.” Inji Tinubu.
Tinubu ya gode wa shugabannin APC da wakilan zaɓen ‘yan takarar da su ka zaɓe shi. Kuma ya ce ya na da yaƙinin APC za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Idan ba a manta ba, Tinubu ya kai ziyarar jajen ambaliya a Jihar Jigawa tare da Abdullahi Adamu, inda har PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa ya bayar da tallafin naira miliyan 50.
Discussion about this post