‘Yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, waɗanda su ka halarci Taron Shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), sun bayyana ɗabi’u da halayen wanda ya cancanta a zaɓa a shugabancin Najeriya a 2023.
Shugaban Da Ya Dace Da Najeriya, Daga Bakin Atiku Abubakar Na PDP:
A wurin taron wanda ya gudana a Legas, ɗan takarar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga masu zaɓe su zaɓi “ƙwararre, mai gogewa wanda ya san ƙabli da ba a din tafiyar da mulki. To mu kuwa mun yi a baya, an ga gogewar mu. Tilas mu yi irin wannan gogewa idan aka zaɓe mu a 2023.” Inji Atiku.
“Mulkin APC bai tsinana wa Najeriya komai ba, sai ƙashin-tsiya ba ƙashin-arziki ba. Wannan mulki ya ƙara rura wutar rabuwar kawuna a Najeriya. Za mu gyara tattalin arziki, magance tsaro, haɗa kan jama’a da sake fasalin mulki a ƙasar nan.”
Shugaban Da Ya Dace Da Najeriya, Daga Bakin Kashin Shettima:
“Babu wanda ya dace da Najeriya a 2023, sai wanda lokacin da ya na Gwamnan Legas ya bunƙasa tattalin arzikin jihar har ya yi ƙarfi daidai na manyan ƙasashen Afrika da ake tutiya da su. Wanda ya dace a zaɓa shi ne shugaban da ke da basira da nagartar iya maida tattalin arziki jiha har ya yi gogayya da na ƙasashen duniya. Idan ya zama shugaban Najeriya kuwa, kowa zai gamsu da irin ci gaban da zai samar.”
Shugaban Da Ya Dace Da Najeriya, Daga Bakin Peter Obi:
“Wanda ya dace a zaɓa a 2023, shi ne ɗan takarar da ke da hangen nesa, wanda zai iya, kuma mai karfin iya yin abin da ake so a yi ɗin.”
Shugaban Da Ya Dace Da Najeriya, Daga Bakin Adebayo Na SDP:
“Masu zaɓe su tsaya su darje, su zaɓi wanda su ka san zai hana shugabannin jama’a ɗirka satar dukiyar al’umma.”
Shawarwarin ‘Yan Takara Wajen Dabarun Hana Naira Durƙushewa:
Atiku, Shettima, Obi, Adebayo sun baje siddabaru a Taron Lauyoyin Najeriya.
Fitattun ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sun bajekolin hanyoyin da su ke ganin za a iya bi domin a hana naira ci gaba da karyewar darajar da ta ke yi a idon manyan kuɗaɗen waje.
Sun bayar da waɗannan shawarwarin ne a ranar Litinin, wuri taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), karo na 62 a Legas.
Faɗuwar darajar naira dai na ci gaba da yi wa tattalin arzikin Najeriya babbar barazanar da tun ana fama da targaɗe, har an kai ga gurguntaka ɗungurugum.
Yayin da Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP, Adebayo ba SDP da Dumebi Kachikwu na ADC su ka halarci gayyatar da aka yi masu, su kuwa Bola Tinubu na APC sai ya tura mataimakin takarar sa, Kashim Shettima ya wakilce shi.
Laƙanin Adebayo, Ɗan Takarar SDP:
“Idan ana so naira ta yi daraja har tattalin arzikin Najeriya ya yi ƙarfi da inganci, to Babban Bankin Najeriya CBN ya daina bai wa abokan ma’aikatan bankin canjin dala misali kamar dala miliyan 30 a farashin gwamnati, su kuma su na zuwa kasuwar ‘yan canji su na sayarwa a farashin ‘yan bumburutu.
“Sannan kuma ban da dalilin da zai sa mai shigo da kaya daga waje, ko masu ‘super markets’ su riƙa cin ƙazamar riba fiye da kamfanin da ya ƙera kayan ko manomin da ya noma amfanin gonar ba.”
Laƙanin Peter Obi, Ɗan Takarar LP:
“Matsawar ana so a samar wa naira daraja a cikin ƙasa da idon duniya, sai fa idan Najeriya ta tashi daga ƙasar ‘yan-cima-zaune ta koma ƙasar da ke sarrafa kayayyakin da duniya ke buƙata.
“Ba za ta taɓa inganta tattalin arzikin ka ba in dai duk abin da ka samu ko ka sayo cinyewa za ka yi ba. Sai ka fa tashi ka na ƙera abin da tilas a zo a saya a wurin ka. Ta nan za a samu kuɗin inganta tattalin arzikin ƙasar ka.”
Laƙanin Kashim Shettima, Mataimakin Takarar APC:
“Wannan matsala daɗaɗɗiya ce, kuma idan ana so a inganta darajar naira da bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, to tilas sai an faɗaɗa hanyoyin samar da kuɗin shiga. Saboda sai da isassun kuɗaɗe ake iya Inganta tattalin arziki.
“Yan hanyoyin samun kuɗaɗen shigar da Najeriya ke tinƙaho da su a yanzu, cike su ke da algusshu, rashawa, wawura, harƙalla da rashin iya tafiyar da tsari.”
Laƙanin Atiku Abubakar, Ɗan Takarar PDP:
“Za daɗe ana tuma tsalle a wuri ɗaya, maimakon a riƙa gudu, muddin ba a soke tsarin farashin canjin dala a bankuna daban da na kasuwar ‘yan canji ba.
“Idan farashin dala a hannun gwamnati ya sha bamban da na kasuwar ‘yan canji, to bumburutu ba zai taɓa barin naira ta yi daraja ba. Sai dai ta koma kamar takardar tsire.”
Discussion about this post