Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu, ya nuna damuwa da takaicin yawaitar garkuwa da mutane da ake yi a faɗin jihohin Kudu maso Gabas, ciki kuwa har da yankin da ya ke wakilta, wato Shiyyar Abiya ta Arewa, a Jihar Abiya.
Da ya ke jawabi wurin rangadin duba-garin kayan inganta rayuwar karkara da ya samar a mazaɓun da ya ke wakilta, Kalu ya ce lamarin ya yi muni sosai, har ya na neman gurgunta tattalin arzikin yankin.
“Zan gayyato sojoji su narka bama-bamai a cikin dajin da masu garkuwa ke ɓoyewa. Saboda haka tun da wuri ma iyayen yara su gargaɗi ‘ya’yan su su daina shiga daji. Domin idan sojoji su ka zo su ka fara ɓarin wuta a cikin dazukan, ko kiyashi ba zai tsira da ran sa ba.”
Kalu ya yi wannan kalami a Ƙaramar Hukumar Umunneochi, inda ya ce za a kakkaɓe duk wani mai kawo wa tsaro ƙalubale da kuma cikas.
A shafin sa ma na Tiwita ya ce, “Nan da watanni huɗu Shugaba Muhammadu Buhari zai ba ku mamaki. Zai sa sojoji su kakkaɓe dazukan Kudu maso Gabas da dukkan mugaye masu garkuwa da mutane da ke ɓoye a cikin dajin.”
A wurin ziyarar kuma ya ce, “Ba za mu lamunci ci gaba da garkuwa da mutane a dajin Ƙaramar Hukumar Umunneochi ba. Ba za mu yarda da masu garkuwa da dajin Ohafia da dajin Ƙaramar Hukumar Arochukwu da na Ƙaramar Hukumar Bende da ma na sauran faɗin jihar Abiya.”
Haka nan kuma Kalu ya nuna damuwa kan yadda tashe-tashen hankula ke ƙara ƙamari a jihohin ƙabilar Igbo.
“Bai kamata a zuba idanu a bari haka kawai wasu tsageru na ƙaƙaba wa ‘yan kasuwa dokar hana fita buɗe kasuwa ba. A duk ranar da mutanen mu ba su fita kasuwa ba, su kan yi asarar naira biliyan 25. Saboda haka wannan shegantaka ba za mu zuba mata idanu ba.
“A Jihar Abiya abin da ke faruwa babu daɗi. Idan ni ne gwamna da tuni aikin Gama ya gama.” Inji Kalu, wanda ya ce sojoji za su koma su ci gaba da aikin sharar ɓatagari a cikin dazukan, cikin watan Nuwamba mai zuwa.”
Discussion about this post