Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya samu kan sa cikin wani matsanancin hali, tsakiyar wutar rikici da sabanin da ya faru tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.
Wannan rikici dai ya kawo wata babbar ɓaraka ga PDP da kuma Atiku, daidai lokacin da ake ƙoƙarin fara shirin kamfen ɗin zaɓen 2023.
Rikicin ya ƙara muni a ranar Laraba, yayin da manyan makusantan Wike biyu, Gwamna Samuel Ortom na Benuwai da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose su ka fito su ka ce faufaufau ba za su goyi bayan takarar Atiku ba.
Yayin da Ortom ya ce har yanzu zuciyar sa ba ta kwanta da goyon bayan Atiku Abubakar ba, Fayose kuwa cewa ya yi Wike ba zai goyi bayan Atiku ba.
Yayin da ɓangarorin biyu ake ganin su na jin haushin Atiku ne saboda ƙin ɗaukar Wike a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, inda ya ɗauki Ifeanyi Okowa Gwamnan Delta, binciken PREMIUM TIMES ya nuna babban dalili shi ne Shugaban PDP Iyorchia Ayi.
Ɓangaren Wike na cewa Ayu ya sauka a naɗa shugaban jam’iyya daga kudu.
Sun ce tunda ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga Arewa, to Ayu ma tunda ɗan Arewan ne, ya zama wajibi ya sauka a miƙa mulkin jam’iyyar PDP a kudu.
To amma shi Atiku bai yarda ba, ya ce a bar Ayu ya ci gaba da shugabanci, har bayan zaɓen 2023.
Ɗaya daga cikin manyan makusantan Wike ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai yarjejeniyar da aka cimma bayan an zaɓi Ayi shugaban PDP.
“An yi yarjejeniya cewa idan a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa na PDP daga Arewa, to Iyorchia Ayu zai sauka daga shugabancin jam’iyya, domin shi ma ɗan Arewa ne, daga Benuwai.” Inji majiyar, wanda ya ce sai a zaɓi shugaban PDP daga Kudu kenan.
Yadda ‘Yan Arewa Su Ka Mamaye Manyan Muƙamai A PDP:
Zaɓen Atiku matsayin ɗan takara ya sa a yanzu cancak PDP ta koma hannun ‘yan Arewa. Atiku ne ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa maso Gabas. Iyorchia Ayu Shugaban PDP da Arewa ta Tsakiya. Walid Jibrin Shugaban Dattawa daga Arewa ta Gabas. Mataimakin Shugaba na Arewa, Umar Damagum ke kasancewa tamkar mataimakin shugaban jam’iyya. Shi ke bayan da umarni idan Ayu ba ya nan.
Yayin da Atiku ya kai wa Wike ziyara bayan kammala zaɓen fidda-gwani, Wike ya tunatar da shi yarjejeniyar da ta ce idan ɗan Arewa ne ya yi nasarar fidda gwani, to Iyorchia Ayu zai sauka daga shugabancin PDP.
Atiku shawarci Wike cewa to su bar wannan batun tukunna a tsakanin su, kada su fitar da shi har sai ya shawarci Ayu ɗin ya sauka tukunna.
“Amma abin takaici sai kawai ji mu ka yi ana cewa Atiku ya ce wa Ayu Wike na so ka sauka daga shugabancin jam’iyya. A lokacin kuwa shi Wike bai sanar wa kowa wannan batun ba.” Inji majiyar mu ya cikin gida.
“Wato so su ke yi su ci gaba da riƙe komai su mayar da kudu saniyar-ware a cikin PDP.”
Wasu kuma na cewa Wike ya fusata da Ayu bayan da Ayu ɗin ya kai wa Gwamna Tambuwal na Sokoto ziyara washekagarin zaɓen fidda-gwani a Abuja.
A lokacin ziyarar ce Ayu ya bayyana cewa Tambuwal shi ne gwarzon taron gangamin PDP, saboda ta dalilin tuggun da ya shirya ne Atiku ya yi nasara, Wike ya zo na biyu.
Idan ba a manta ba, Wike ya ragargaji Tambuwal da sauran waɗanda su ka goyi bayan Atiku a wurin, inda washegarin zaɓe ya kira su maciya amanar da ba su cancanci a sake ba su riƙon amana ba.
Tuni dai Wike na ci gaba da ganawa da wasu ‘yan takarar shugaban ƙasa na wasu jam’iyyu, irin su Peter Obi na LP, Rabi’u Kwankwaso na NNPP.
Discussion about this post