Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa abinda ya fi dace wa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ya yi shine ya hakura ya zo ya bi shi kawai ya tsaya masa mataimakin shugaban kasa.
Kwankwaso ya kara da cewa ” Nine NNPP idan na fice jam’iyyar zata mutu murus, maimakon haka ya kamata a shine Obi ya biyo ne NNPP ya zo mu yi takara kawai.
” Ko da muka zauna muka tattauna, ƴan ɓangaren Obi sun ce nine ya zama mataimakin shugaban kasa. Amma kuma hakan zai yi sanadiyyar rugujewar NNPP.
Kwankwaso ya kara da cewa ” Ƴan yankin Kudi Maso Gabas, wato Inyamirai, sun iya kasuwanci matuka amma kwamɓar suke a siyasa. Ba su iya siyasa ba. Suna can kasa.
” Dole sai sun fito sun koyi siyasa, zamantakewa idan ba haka a kullum za su rika kasancewa a can kasa ne a siyasa.
Idan suka hakura suka bi NNPP, bayan haka idan aka samu nasara sai suma su zarce kujerar shugaban kasa. Abin a hankali da lissafi ake yi ba da baki ba.
Idan ba a manta ba, Kwankwaso da Peter sun gana domin tattauna yadda za su iya haɗe wa domin fafatawa da APC da PDP a zaɓen 2023.
Sai dai kuma abin kamar da wuya domin dukkan su babu wanda zai iya hakura wa ɗaya domin a samu nasara a zaɓe.
Discussion about this post