Ɗan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya karyata rahoton cewa wai wani kwamitin PDP ta zaɓi gwamnan Ribas Nysome Wike a matsayin mataimakin sa a zaben shugaban kasa dake tafe.
Atiku ya ce kwamitin da aka naɗa sun zaɓi wasu mutum uku ne wanda a ciki zai zaɓi mutum ɗaya ya yi masa mataimakin shugaban kasa.
Idan ba a manta ba Atiku ya zaɓi gwamnan Delta Okowa a matsayin wanda zai tsaya masa takarar mataimakin shugaban kasa.
Tun bayan haka gari ya ɗau zafi da ya sa wasu da dama daga cikin jigajigan PDP suka koma gefe, wato suka tsame hannun su daga tafiyar Atiku ɗin.
Ba su dai fice daga jam’iyyar ba amma kuma sun nisanta kan su daga tafiyar Atiku da Okowa.
Atiku ya ƙara da cewa ya zaɓi Okowa ne saboda kasancewa shi mutum natsatsse sannan mai kishin Jam’iyya da mutanen Najeriya.
Gwamnan Benuwai Emmanuel Ortorm ya fusata bayan Atiku ya zaɓi Okowa cewa dagangar ya ki ɗaukar Wike saboda son rai, amma kuma su kwamitin da jam’iyyar ta kafa Wike suka zaɓa mataimakin shugaban kasa.
Haka shima Wike ɗin ya ke yarda su haɗa ido da Atiku, sannan baya halartar duk taron da Atiku ya halarta na jam’iyyar, kamar Kamfen da suka yi kafin zaɓen Osun wanda jam’iyyar ta yi nasara.
A karshe dai Atiku ya ce zai cigaba da ganawa da waɗanda suka fusata da shi kan sa Wike.
Discussion about this post