Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta tsakiya ya lallasa ƴan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a garin Kaduna ranar Alhamis.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen a Kaduna, malamin zaɓe Anachuna Izu, ya sanar cewa sanata Uba ya samu zunzurutun kuri’u 1, 149.
Wanda ya zo na biyu a zaɓen Bashir Abubakar ya samu kuri’u 37.
Honarabul Sani Shaaban ya samu kuri’u 10 kacal ne a zaben.
Da yake jawabi bayan kammala sanar da sakamakon zaɓen, sanata Uba ya mika godiyar sa ga gwamna Nasir El-Rufai bisa goyon baya da yake bashi da kuma jam’iyyar APC a jihar.
Uba ya ce zai mika hannun gayyatar sa ga sauran ƴan takarar da ya lallasa su zo a haɗa hannu domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓuɓɓuka dake tafe.
” Bwbu abinda zan ce muku wakilan jam’iyyar mu ta APC sai dai godiya da yi muku fatan Alkhairi. Ina godiya kuma ina fatan wannan tafiya za mu yi tare har zuwa Allah ya bamu nasara a babban zaɓuka masu zuwa.
” Sannan kuma zan tuntuɓi sauran ƴan takara da muka fafata da su a wannan zaɓe su zo a haɗa hannu domin cigaban jam’iyyar a jihar Kaduna baki ɗaya.
A karshe Uba ya cigaba da mika godiyarsa ga gwamna El-Rufai yana mai cewa ” Muna nan za mu cigaba da yi maka biyayya domin cigaba da kwankwadar ruwan lagwada daga koramar arziki da baiwa masu ɗimbin yawa da Allah yayi maka. Muna godiya da irin jagorancin da kake mana gaba ɗayan mu a jihar da jam’iyyar mu ta APC.
Discussion about this post