Sakamakon zaɓukan fidda gwani na ƴan takarar gwamna da aka yi a jihohin kasar nan.
Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa Aishatu Binani ce ta yi nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka yi a jihar Adamawa ranar Alhamis.
Binani ta kada tsohon shugaban hukumar EFCC ta kasa, Malam Nuhu Ribadu.
Binani ta samu kuri’u 430, Ribadu 288 sai kuma tsohon gwamna Bindow da ya samu kuri’u 103. Abdulrazaq Namdas ya samu kuri’u 94.
A jihar Kebbi Nasir Idris ne ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar na jam’iyyar APC inda Nasiru Gawuna yayi nasara a zaɓen Kano.
Gawuna zai fafata Abba Gida-Gida na jam’iyyar NNPP, da Mohammed Abacha na jam’iyyar PDP.
Gawuna ya samu kuri’a 2289. Sha’aban Sharada ya samu kuri’a 30.
Haka kuma a jihar Katsina Dikko Rada ne ya yi nasara da kuri’a 506.
Umar Namadi ne ya lashe zaben fitar da gwanin jihar Jigawa bayan ya samu ƙuri’u 1,220.
Namadi ya kada Ibrahim Hadejia, Faruk Adamu da Sabo Nakudu.
A jihar Gombe kuwa, gwamna Inuwa Yahaya ne ya yi nasara zaben gwamnan ba tare da hamayya ba kamar yadda Babagana Zulum na Barno shima yayi nasara a zaɓen Jihar Barno.
Mai mala Buni na Yobe ne yayi masara azaɓen fidda gwanin jihar.
Bauchi
A Jihar Bauchi kuwa, tsohon babban hafsan sojojin saman Najeriya Saddique Abubakar ne ya yi nasara a zaben fitar da gwani bayan ya kara da Nura Manu Soro da Sanata Halliru Jika da Musa Babayo.
Haka kuma akwai Honourabul Farouk Mustapha da Mahmood Maijama’a da Farfesa Muhammad Pate wanda ya fafata da su duka a zaɓen.
A jihar Kaduna Sanata Uba Sani ne ya ya nasara a zaɓen fidda gwanin.
Ya kada surikin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Sani Sha’aban a zaɓen.
A jihar Nasarawa gwamna Sule Abdullahi ne yayi nasara a zaben fidda gwani na APC.
A jihar Neja kuma ɗan majalisa Umar Bago ne yayi nasara a zaɓen gwamna na jihar.
Bago ya doke Mohammed Malagi, shugaban jaridar Blueprint.
Bago ya samu kuri’u 540, Malagi kuma kuri’u 386.
Mataimakin gwamnan jihar Mohammed Ketso ya tashi da kuri’u 17 ne kacal.
Discussion about this post