Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da jam’iyyar APC za ta iya afkawa cikin ruɗanin da zai iya sa ta rasa jihar ga jam’iyyar adawa, wato jam’iyyar PDP.
Babban matsalar da za ta iya afkawa ciki kuwa shine wajen zaɓen ƴan takara musamman kujerar gwamna.
Abin da ya shige wa mutane da dama duhu a jihar shine ganin yadda sanata Uba Sani, wanda ɗan gaban goshin gwamna El-Rufai ya fito takara sannan shima tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Mohammed Sani Dattijo ya fito kuma dukkan su da gaske suke.
” A gani na banga dabara ba ko kuma in ce hikima a ciki na barin makusantan sa su rika kamfen haka bayan za ka iya tara su tun farko ka haɗa kansu a zaɓi daya da zai fafata da sauran a wajen zaɓen fidda gwani. Bayan kashe kuɗi da kowannen su ke yi takamarsa shine daga ƙarshe shine El-Rufai zai zaɓa don a mara masa baya.” Sani Lawal, mai sharhi akan siyasa.
Idan ka yi zurfin tunani da hange mai nisa, zaka ga lallai fa za a samu matsalar gaske a lokacin da za ayi zaben fidda gwani.
Ana ganin idan dai El-Rufai ya ce Uba Sani ya hakura ya sauka wa Dattijo, anya hakan zai yiwu kuwa, bayan ganin irin bautar da yayi wa siyasar Kaduna da APC da kuma irin gudummawar da ya baiwa shi kansa gwamnan jihar wato ubangidan sa a tsawon mulkin sa yanzu shekara 7 kenan.
Idan kuma Dattijo ne zai hakura toh, kila hakan ya yi wa jam’iyyar tasiri ganin wannan shine karon farko da ya fito takara irin haka, bai goge ba tukunna. Kila umartarsa ya janye wa sanata Uba ya fi yi wa jam’iyyar tasiri a zaben game gari.
Sai dai kuma jihar Kaduna na bukatar wanda zai iya cigaba da irin ayyukan da gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi ne.Mutumin da bashi da tsoro, gogagge wanda takawa ne kawai ke gaban sa da ayyukan raya kasa da cigaban jihar ba daɗaɗa wa wasu rai ba.
Idan ko haka ya ke so toh tabbas wasu na gani Dattijo ne ya fi dacewa ya mara wa baya domin a samu haka.
Baya ga Uba Sani da Mohammed Sani Dattijo akwai wasu jigajigan da suka fito takara wanda suma za a iya fafatawa da su, da idan shi kansa El-Rufai bai maida hankali ba wani daga cikinsu zai iya yi musu shigan ba zata ya yi nasara a ɗauke tiket din APC din wato ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC ɗin.
Akwai Bashir Jamoh, wanda hamshakin attajiri ne kuma yana da goyon bayan wasu gaggan ƴan siyasa a Abuja. Shima ya fito kuma da gaske yake yi.
Haka kuma Sani Sha’aban sirikin shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Ya fito kuma shima da gaske ya ke yi.
Akwai kuma tsohon shugaban hukumar Alhazai ta kasa, Mohammed Abdullahi dukkan su suna son wakilan APC su tsai da su ɗan takarar gwamnan jihar.
A halin yanzu idan har El-Rufai da makusantan sa dake takarar gwamnan jihar basu yi gaggawar daidaita kansu ba su mara wa ɗayan su baya, to lallai za a yi kare jini biri jini ne a wajen zaɓen fidda ƴan gwani inda wani can zai iya tsintar ‘dami a kale’ su kuma su rasa.
Jam’iyyar PDP a Kaduna
A nasu ɓangaren jam’iyyar PDP ita ma tana cukuikuye ne cikin ruɗani da hargowar ƴan takara da suka fito da yawan su.
A wannan karon akwai yiwuwar fitaccen ɗan takaran su Isah Ashiru wand shine jam’iyyar ta tsayar a wancan karon ta samu matsala ganin irin ƴan takaran da suka fito neman tikitin kujerar.
Gagga daga cikin su kuwa sun haɗa da Haruna Saeed tsohon Akanta Janar ɗin gwamna Makarfi, akwai Sanata Datti Babba-Ahmed, Sanata Shehu Sani, Sani Sidi da sauran su. Suma idan ba su yi da gaske ba wajen sasanta ƴan takara ba za ta iya ɓarewa da su.
Discussion about this post