Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta damke wata dillaliyar muggan kwayoyi mai suna Jamila Abdullahi mai shekaru 30 a jihar.
Jamila mazauniyar kwatas din Kwanar Ungogo ne dake karamar hukumar Ungogo.
Jami’an tsaron sun samu bayanin cewa Jamila ita ce babban dillaliyan shalasho a karamar hukumar Ungogo da kewaye.
bayan ta shiga hannun ‘yan sanda Jamila ta bayyana cewa ita bazawara ce sannan ta dauki sama da shekaru biyu tana siya da siyar da shalasho.
Ta ce lokacin da ‘yan sanda suka fara kamata a karon farko ta daina siyar da shalasho amma sai ta ci gaba bayan wani lokaci.
Jamila ta ce tana siyan shalasho sari a wurin wani mutum amma bayan ya samu labarin cewa ‘yan sanda sun kama ta sai ya gudu ya bar kasar.
Kwamishina Dikko ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike inda bayan an kammala za a kai Jamila kotu.
Ya shawarci dillalai da masu ta’ammali da muggan kwayoyi su tuba su daina abinda suke yi ko kuma su tattara su fice daga Kano kwata-kwata.
Rundunar ‘Operation Puff Adder’ za ta ci gaba da aiki a jihar saboda nasarorin da take samu wajen kama batagari a jihar.
Dikko ya yi kira ga mutane da su ci gaba da yi wa jihar da kasa Najeriya addu’a sannan su guji daukar doka a hannunsu.
Ya ce da zaran sun ga wani abin da basu yadda da shi ba, su gaggauta kawo kara ofishin ‘yan sanda.