Hukumar Daƙile Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi, NDLEA ta kama wata mata mai shekaru 59, wadda aka tabbatar ita ce shugabar dillalan muggan ƙwayoyi a Jihar Delta da maƙwautan jihohi.
Matar mai suna Bridget Emeka, an fi sanin ta da suna Mama. An kama ta ne a ranar Lahadi, a wani danƙareren gidan ta da ke Warri a jihar Delta.
Kakakin Yaɗa Labaran NDLEA, Femi Babafemi ne ya sanar da haka a ranar Talata a Abuja.
NDELA sun zargi Mama da riƙa yin amfani da kantamemen gidan ta da ke kan Titin Favour, Unguwar Otukutu da ke yankin Effurun a Warri ta na ta dafa sankacen hodar koken da sauran muggan ƙwayoyi ta na raba wa dillalan ta.
A lokacin da aka kama ta, jami’an NDLEA sun tarkata har da ma’aikatan da makusanta su 9 duk ta yi awon-gaba da su.
NDLEA ta ce an samu nasarar yin wannan samamen kamun manyan ‘yan ƙwayar tare tafiya tare da sojoji wajen yin kamen.
Babafemi ya ce gidan Mama ƙaton gida ne da masu tu’ammali da ƙwayoyi ke kwana kuma ana amfani da gidan a matsayin wurin tara muggan ƙwayoyi ana rarraba wa manyan diloli a cikin Warri.
Baya ga muggan ƙwayoyi da aka kama a gidan, an samu bindiga 1 mai harsasai 15.
“An samu takardun bayanai, motoci biyu, wayoyin selula da sauran tarkacen wuraren da ake zuba ƙwatoyi da ledojin naɗe ƙwaya duk a cikin gidan.
Ya ce ana nan ana ci gaba da binciken da idan an kammala za a maka su kotu.
Discussion about this post